Zaben Kananan Hukumomi: Gwamnan Arewa Ya Ba Da Hutun Kwana Daya

Zaben Kananan Hukumomi: Gwamnan Arewa Ya Ba Da Hutun Kwana Daya

  • Gwamnatin jihar Neja ta bayyana ranar Alhamis, 10 ga watan Nuwamba a matsayin hutu
  • Gwamna Sani Bello ya bayar da hutun ne domin ba mazauna jihar damar komawa yankunansu don kada kuri'a a zaben kananan hukumomi da za a yi a fadin jihar
  • Babban sakataren gwamnatin jihar Ahmed Matane ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar

Niger - Gwamnan jihar Neja, Sani Bello, ya ayyana ranar Alhamis, 10 ga watan Nuwamba, a matsayin hutu don gudanar da zabuka a kananan hukumomi 25 da ke jihar, jaridar Punch ta rahoto.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Ahmed Matane, ya saki a garin Minna, babban birnin jihar.

Gwamna Sani Bello
Zaben Kananan Hukumomi: Gwamnan Arewa Ya Ba Da Hukun Kwana Daya Hoto: Punch
Asali: UGC

Manufar bayar da hutun

Matane ya bayyana cewa hutun zai baiwa al'ummar jihar damar kada kuri'unsu a zaben.

Kara karanta wannan

Dan Takarar Gwamnan PDP a Zamfara Ya Fusata, Ya Yi Kakkausan Martani Kan Hukuncin Kotu

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sakataren gwamnatin ya kuma bayyana cewa kasuwanni da ofishoshi za su kasance a kulle yayin zaben sannan za a takaita zirga-zirga mutane da ababen hawa illa wadanda ke ayyuka masu muhimmanci, rahoton Nigerian Tribune.

Ya ce:

"Gwamnati na umurtan jama'a da su fito sannan su sauke hakokinsu na yan kasa a ranar Alhamis. Wannan sabuwar dama ce ta zabar wakilai da shugabanni wadanda ake sa ran zasu yi aiki da burinmu na yin hadaka a matakin karamar hukuma."

Bello ya kuma umurci duk hukumomin tsaro a jihar da su tabbatar da zabe cikin lumana, yana mai cewa gwamnati ta jajirce don bayar da kariya da tabbatar da ganin tsarin ya gudana cikin lumana.

Yadda jama'a suka shirya ma zaben

Legit.ng ta tuntubi wasu mazauna jihar don jin yadda suka shirya ma wannan zabe inda da yawansu suka nuna cewa tuni sun garzaya yankunansu domin ganin sun amfani da yancinsu na yan kasa.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC: Kotu za ta tabbatar ban fadi zabe ba, za a dawo min da kujera ta

Wata ma'aikaciyar gwamnati mai suna Amina Muhammad ta ce:

"Yanzu haka na bar Minna ina Edotun domin kada kuri'ata. Ba zan bari a bar ni a baya ba wannan karon domin ina muradin ganin dan takarata ya lashe zabe. Ina son ganin sauyi a karamar hukumata."

A bangarensa, mallam Abubakar ya ce suna fatan ganin an yi zabe cikin lumana domin zaben karamar hukuma na da karfi kusan an fi daukarta da zafi.

Ya ce:

"Babban burinmu da addu'anmu shine ayi zabe lafiya cikin lumana kuma muna rokon Allah ya baiwa mai rabo sa'a sannan ya bamu jagorori da za su yi mana hidima tsakaninsu da Allah ba masu son zuciya ba.
"Gaskiya jihar Neja na tsananin bukatar shugabanni a dukkan matakai domin abubuwa basa tafiya yadda ya kamata a bangarori da dama amma muna sa ran samun sauki nagari da yardar Allah."

Asali: Legit.ng

Online view pixel