2023: Tinubu Ya Zabi Babban Jiha A Arewa Don Kadamar Da Kamfen Dinsa

2023: Tinubu Ya Zabi Babban Jiha A Arewa Don Kadamar Da Kamfen Dinsa

  • Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na Tinubu/Shettima ta zabi jihar Plateau don kaddamar da kamfen
  • Jam'iyyar mai mulki a kasa ta ce za ta kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasar nata a ranar 15 ga watan Nuwamban 2022
  • Jam'iyyar kuma ta shirya tuntubar masu ruwa da tsaki na kasashen ketare daga ranar 4 zuwa 10 ga watan Disamban 2022

FCT, Abuja - Jam'iyyar All Progressives Congress, APC, ta tsayar da ranar 15 ga watan Nuwamban 2022, don kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasarta a Jos, babban birnin jihar Plateau.

Hakan na cikin jadawalin da jam'iyyar ta fitar ne a ranar Laraba 3 ga watan Nuwamban 2023, The Punch ta rahoto.

Buhari, Tinubu, Adamu
APC Za Ta Kaddamar Da Kamfen Din Shugaban Kasa A Jihar Plateau. Hoto: @MobilePunch.
Asali: Twitter

Hakan na zuwa ne makonni bayan hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta amince da fara yin kamfen na zaben 2023.

Kara karanta wannan

2023: Nasarar APC Na Cikin Haɗari, In Ji Shugaban Kamfen Na Adamawa

Jam'iyyar ta APC, a lokuta da dama ta yi yunkuri fara yakin neman zaben amma ta dage saboda wasu dalilai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amma, a jadawalin da kwamitin kamfen din dan takarar shugaban kasar ta fitar a ranar Laraba, jam'iyyar za ta fara yakin neman zaben shugaban kasarta a Jihar Plateau, yayin da za a fara tarukan sauraron ra'ayi tare da masu ruwa da tsaki a sassan kasar daga 16 zuwa 30 ga watan Nuwamba.

Sauran ababen da jam'iyyar ta fitar a jadawalin zaben na 2023

Jam'iyyar kuma ta shirya tuntubar masu ruwa da tsaki na kasashen waje daga ranar 4 zuwa 10 ga watan Disamban 2022.

A ranar 8 ga watan Fabrairun 2023, za a yi tattaki da bikin wakoki a birnin tarayya, Abuja, yayin da taron da za a yi na Legas shine na karshe a ranar 13 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Jam'iyyar APC Ta Saki Jadawalin Yakin Neman Zabenta Na Shugaban Kasa

Jam'iyyar ta kara da cewa kwamitin zaben za ta yi amfani da ranar 12 zuwa 24 don 'tsara zabe' gabanin babban zaben 2023.

2023: Tinubu, Obi ko Atiku? Bincike Ya Nuna Wanda Zai Ci Zaɓen Shugaban Ƙasa, An Bayyana Abin Da Zai Faru

An yi hasashen cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu ne zai lashe zaben shugaban kasa da ke tafe a Najeriya, Vanguard ta rahoto.

Legit.ng ta rahoto cewa kamfanin Fitch Solutions Country Risk and Industry Research ta yi wannan hasashen a sabuwar rahoton ta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel