Jerin Sunayen Shugabannin Yarbawa Da Suka Hallara Yayin da Tinubu Ya Samu Goyon Bayan Shugaban Afenifere
- Dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu ya ziyarci gidan Pa Reuben Fasoranti, shugaban Afenifere na kasa, a Akure, babban birnin jihar Ondo a ranar Lahadi
- Farosanti ya tarbi tsohon gwamnan na jihar Lagas wanda ya gabatar da manufofinsa a gabansu hannu bibbiyu sannan ya saka masa albarka
- Wasu manyan shugabannin Yarbawa da suka hada gwamna, mataimakan gwamnoni, sanataoci da shugabannin Afenifere sun hallara a wajen
Ondo – Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ya gana da shugaban kungiyar kare muradin Yarbawa, Pa Reuben Fasoranti, a ranar Lahadi, 30 ga watan Oktoba.
Jaridar The Nation ta rahoto cewa tsohon gwamnan na jihar Lagas ya kai ziyarar bangirma ga dattijon kuma ya samu tabbaraki a gidan Fasoranti da ke Akure, babban birnin jihar Ondo.

Asali: UGC
Wasu manyan shugabannin Yarbawa da manyan masu fada aji na Afenifere sun hallara a wajen tattaunawa da kungiyar.
Shugabannin da suka hallara sun hada da:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Biodun Oyebanji, Gwamnan jihar Ekiti
Archbishop Ayo Ladigbolu
Farfesa Isaac Adewole
Oba Olu Falae
Otunba Gbenga Daniel
Janar Alani Akinrinade
Janar Olu Bajowa
Mista Sola Iji
Dr Kunle Olajide
Sanata Cornelius Adebayo
Bashorun Seinde Arogbofa
Sanata Iyiola Omisore
Cif Bisi Akande
Dare Babarinsa
Cif Pius Akinyelure
Mataimakin gwamnan Oyo Bayo Lawal
Mataimakin gwamnan Ondo Aiyedatiwa.
Cif Segun Adesegun, ya wakilci tsohon gwamna Segun Osoba
Sanata Tony Adefuye
Sanata Dayo Adeyeye Shugabannin Afenifere na jiha da wasu da dama.
Tinubu Ya Isa Akure Don Ganawa Da Shugabannin Afenifere
A baya mun kawo cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) Asiwaju Bola Tinubu, ya isa Akure, babban birnin jihar Ondo.
Tinubu wanda ya isa jihar a yau Lahadi, 30 ga watan Oktoba, zai gabatar da manufofinsa ga Pa Reuben Fasoranti da shugabancin kungiyar Yarbawa ta Afenifere, jaridar The Nation ta rahoto.
Tsohon gwamnan na jihar Lagos ya samu tarba daga gwamnan Ekiti, Abiodun Oyebanji, mataimakin gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, da sauran shugabannin APC, rahoton Punch.
An tsaurara matakan tsaro a kewayen gidan Pa Fasoranti da ke Akure yayin da mambobin APC ke tururuwan zuwa yankin don yiwa Tinubu maraba da zuwa.
Asali: Legit.ng