Buhari Yayi Magana Akan Batutuwan Tsaro da Amurka, Burtaniya da Sauransu Ke Yi Kan Abuja

Buhari Yayi Magana Akan Batutuwan Tsaro da Amurka, Burtaniya da Sauransu Ke Yi Kan Abuja

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yabawa jami'an tsaron Najeriya bisa kokarin da suke na wanzar da zaman lafiya
  • Shugaban ya kuma shawarci 'yan Najeriya su kasance a ankare kan gargadin bazaranar tsaro da kasashen turai suka yi kan Abuja
  • Amurka da Burtaniya sun jawo cece-kuce a makon nan tun bayan da suka fara dago batun za a ka hare-haren ta'addanci a Abuja

FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari na Najeriya ya bukaci 'yan Najeriya da su kwantar da hankala, amma su kasance a ankare kan shawarwarin tsaro da kasashen turai suka fara bayarwa kan birnin tarayya Abuja.

A cewar wata sanarwa da Buhari ya fitar ta bakin mai magana da yawunsa, Garba Shehu, ya shawarci 'yan kasa da jami'an tsaro da su zama masu sanya ido kan lamarin tsaron kasar nan.

Kara karanta wannan

Barazanar Tsaro: An Gano Asalin Dalilin Rudewa Amurkawa a Abuja

Shawarin da Buhari ya ba 'yan Najeriya kan lamarin tsaro
Buhari yayi magana akan batutuwan tsaro da Amurka, Burtaniya da sauransu ke yi kan Abuja | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Idan baku manta ba, a makon nan ne kasar Amurka ta ba 'ya'yanta shawarin fara barin Najeriya sakamakon tsoron barazanar tsaro da ka iya biyo baya a babban birnin tarayya Abuja.

Sun gargadi 'yan kasarsu da su kasance a ankare domin kuwa akwai yiwuwar kai hare-haren ta'addanci a sassan Najeriya, musamman Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amurka ta shawari 'yan kasarta su fara barin Najeriya

Tuni kasar Amurka ta dakatar da wasu ayyuka a ofishinta na jakadanci tare da umartar wasu ma'aikatanta da su gaggauta barin kasar.

Sai dai, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, shawarwarin da Amurka ke bayarwa ba yana nufin za a kai hari ne kai tsaye a Abuja, sai dai don a kula da lamarin.

A bangare guda, shugaban kasa Buhari ya yabawa hukumomin tsaro dake kai komo don ganin an samu mafita ga matsalar tsaro a kasar nan.

Kara karanta wannan

Jami'an DSS da NIA Sun Damke Yan Ta'addan ISWAP 35 A FCT Abuja

Mata Na Ba ’Yan Bindiga ’Ya’yansu Mata Saboda Kudi, Inji Kwamishinar Kaduna

A wani labarin, Hafsat Baba, kwamishinar ayyukan jama'a ta jihar Kaduna ta bayyana cewa, yana da matukar muhimmanci a magance wasu matsaloli da suka dumfaro mata a jihar.

Ta bayyana cewa, akwai matan dake tura 'ya'yansu mata ga 'yan ta'adda saboda kawai su samu kudin kashewa, rahoton TheCable.

Hafsat ta bayyana hakan ne a ranar Laraba 26 ga watan Oktoba a tattaunawa ta 22 na majalisar kasa kan harkokin mata da ya gudana a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel