Barazanar Tsaro: An Gano Asalin Dalilin Rudewa Amurkawa a Abuja

Barazanar Tsaro: An Gano Asalin Dalilin Rudewa Amurkawa a Abuja

  • Manyan dalilan da suka sa ofishin jakadancin Amurka ya umarci ma’aikata su na Najeriya da su tattara komatsansu su har Abuja ya bayyana
  • An gano cewa, tabbas akwai barazanar kai hari amma Amurka ta dauka abun da girma wanda hakan yasa ta gana da ofisoshin jakadancin wasu kasashen Turai a Abuja
  • Wannan kururuta al’amarin da ta dinga wata majiya tace yana da alaka da yadda ta ga gwamnatin Najeriya ta hada alaka da gwamnatocin Chana da Rasha wurin siyan makamai

FCT, Abuja -A farkon makon nan ne ofishin jakadancin Amurka ya yi gargadi kan yuwuwar farmaki a babban birnin tarayya na Abuja.

Barazana
Barazanar Tsaro: An Gano Asalin Dalilin Rudewa Amurkawa a Abuja. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Bayan ofishin jakadancin ya bayar da sanarwa, hukumar Birtaniya ta bayar da shawarin kai da kawowa ga ma’aikatan ta yayin da take sanar da raguwar ayyukanta.

Kara karanta wannan

Jami'an DSS da NIA Sun Damke Yan Ta'addan ISWAP 35 A FCT Abuja

Hakazalika, sauran kasashen Turai kamar su Ingila, Australia, Jamus, Bulgaria, Ireland da Denmark duk sun sanar da rage ayyukansu yayin da zasu dinga mayar da hankali kan na dole a Najeriya.

Daily Trust ta gano daga majiyoyin diflomasiyya cewa, sauran kasashen sun bi sahun Amurka ne bayan jerin taruka, yada bayanan sirri da kuma gamsassun shaidu kan hatsarin dake tattare da birnin tarayyan.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Daya daga cikin majiyoyin tace:

“A makon da ya gabata ne aka kama wani da ake zargin a ofishin jakadancin Amurka a kwaryar Abuja yana leken asiri a farfajiyar. Hakazalika, an samu abubuwa masu fashewa kusa da hanyar shiga gidan wani ma’aikacin Amurka a ranar Asabar, 22 ga watan Oktoba.”

Majiyar ta kara da cewa, bayan tattaro bayanan sirri kan shirin kai farmaki kan ‘yan Amurka da sauran bakin haure, gwamnatin Amurka ta yanke hukuncin aiko jami’anta na musamman Abuja don su duba barazanar.

Kara karanta wannan

Amurka Ta Shawarci Ma'aikatan Ofishinta Su Kwashe Iyalansu Daga Abuja Yanzu

Amma wata majiya daga hukumomin tsaron Najeriya tace wannan tsoron duk bashi da amfani.

“Wannan tsoron na mene ne? Ba wannan bane lokaci na farko da aka fara bada wannan barazanar ba. Me yasa ‘yan Najeriya ke kaunar abubuwan ketare? Saboda sanarwa tazo daga Amurka? Kaunar da muke yi wa abubuwan ketare yayi yawa.
“Idan zaku tuna, a ranakun 19 ga Maris din 2022, 26 ga Afirilun 2022 da 14 ga Disamban 2021, DSS ta fitar da kan kunne kan yunkurin saka bam da hari da wasu ke shiryawa. ‘Yan Najeriya sun musanta tare da kwantar da hankulansu.
“Bayan watanni kadan, Kano, Jigawa, Imo da sauran wurare duk an kai musu hari. Haba! Mutane su kwantar da hankalinsu tare da goyon bayan hukumomin tsaro da bayanai. A saka ido kuma.”

Sai dai, wani babban jami’in tsaro yace gwamnatin Amurka ta zake wurin martani inda yace duk wannan barazanar ana iya magance ta ba tare da yada gutsuri tsoma daga ofishin jakadancin Amurka ba.

Kara karanta wannan

An samu karin kasashe da suka gano yiwuwar kai hare-hare a Abuja da Jihohi 22

Wata majiya ta alakanta yadda gwamnatin Amurka ta dauka lamarin da alakar da ta gani ta kusanci da gwamnatin Najeriya da gwamnatocin China da Rasha balle wurin siyan makamai.

A ranar Alhamis, daya daga cikin manyan kantunan Abuja an rufe shi har sai bata ta gani saboda barazanar tsaron.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel