Gwamna Oyetola Ya Jagoranci Tattakin Kilomita Sama da 9 Don Nuna Goyon Baya Ga Tinubu

Gwamna Oyetola Ya Jagoranci Tattakin Kilomita Sama da 9 Don Nuna Goyon Baya Ga Tinubu

  • Gwamnan jihar Osun ya fito ya jagoranci tafiyar kafa ta tsawon kilomita 9.2km a Osogbo domin nuna goyon bayan Tinubu
  • Dandazon masoyan APC suka taru a gidan gwamnatin Osun da safiyar nan kafin fara tattakin bayan fitowar gwamna da tawagarsa
  • Da yake jawabi bayan tattakin, Oyetola yace bai kamata yan Najeriya su mika Majeriya hannun waɗanda ba su san shugabanci ba

Osun - Gwamnan jihar Osun, Adegboyega Oyetola, mataimakinsa Benedict Alabi da wasu mambobin majalisar zartsawa sun jagoranci dubbannin masoya a Osogbo yayin tattakin nuna goyon baya ga Tinubu/Shettima.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa magoya bayan sun taru ne a gidan gwamnatin Osun dake Oke-Fia, Osogbo da misalin ƙarfe 9:00 na safe kafin daga bisani su tafi tattakin.

Kara karanta wannan

2023: Dalilin Da Yasa Ni da Wasu Gwamnonin PDP Muka Sauya Sheka Zuwa APC, Tsohon Minista

Tattaki domin Tinubu a Osun.
Gwamna Oyetola Ya Jagoranci Tattakin Kilomita Sama da 9 Don Nuna Goyon Baya Ga Tinubu Hoto: @thenationnews
Asali: Twitter

Gwamnan ya jagorancin tafiyar ƙafan ne daga gidan gwamnati aka ratsa ta titin Oke-Fia, Alekuwodo, Ola-Iya, Odi-Olowo, Isale-Osun, Oja-Oba, Titin Station, Ajegunle kana aka datse tattakin a Tashar Freedom.

Magoyan bayan na ɗauke da Banoni sannan sun sanya Hular hana Sallah mai ɗauke da Hoton ɗan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Haka zalika suna tafiya suna rera waƙa domin jawo hankalin mazauna jihar su kaɗa wa jam'iyyar APC kuri'unsu a babban zaɓen 2023 mai zuwa.

Bidiyon Tattakin Gwamna Oyetola

Gwamna Oyetola ya yi jawabi

Da yake jawabi a wurin da aka ɗiga aya a tattakin, Gwamna Oyetola ya ja hankalin magoya bayan su zaɓi Tinubu a zabe mai zuwa kuma su ci gaba da tallata APC.

Gwamnan yace:

"Tinubu zai zama shugaban kasar nan saboda bakuna masu tsarki sun ambaci haka. Ƙaurin sunan Tinubu ya kafu a jihar Osun, tun 1999 yake tare da mu, ya taka rawa wajen nasarar mu."

Kara karanta wannan

Wani Bawan Allah Umar, Ya Fara Tattaki da Kafa Zuwa Abuja Domin Nuna Goyon Baya Ga Tinubu

"Bai kamata yan Najeriya su bar ƙasar nan hannun wasu da basu san komai a shugabnci ba, dole mu zaɓi mutum mai kwarewa. Shi ne asalin wanda ya canza Legas."

A wani labarin kuma Atiku Abubakar Ya Maida Zazzafan Martani Ga Tinubu Kan Kalaman Zama a Dubai

Alhaji Atiku Abubakar, ɗan takarar jam'iyyar PDP a zaɓen 2023 yace ba wanda zai yarda da Tinubu da APC.

Da yake martani kan kalaman Tinubu a Kano ta bakin kakakinsa Paul Ibe, yace mutane na tantama kan abubuwa da dama tattare da ɗan takarar na APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel