Wani Bawan Allah Ya Taso Daga Gombe Zuwa Abuja Saboda Goyon Bayan Tinubu

Wani Bawan Allah Ya Taso Daga Gombe Zuwa Abuja Saboda Goyon Bayan Tinubu

  • Wani matashi ɗan shekara 31, Muhammaed Umar, ya fara tattaki yau Litinin daga Gombe zuwa Abuja don nuna goyon bayan Tinubu
  • Umar, ya shaida wa NAN jim kaɗan kafin fara tafiyarsa cewa ya shirya haka ne domin kaunar da yake wa Tinubu da Shettima
  • A cewarsa, iyalansa na tare da shi ɗari bisa dari kuma suna masa addu'a kan tafiyar da ya yi niyyar yi

Gombe - Wani mutumi ɗan shekara 31 a duniya, Mohammed Umar, a ranar Litinin ya fara tafiyar ƙafa ta tsawon kilomita 425 daga jihar Gombe zuwa birnin tarayya Abuja domin nuna goyon bayansa ga Bola Ahmed Tinubu na APC.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Umar mamba ne a ƙungiyar masoyan Tinubu ɗa Shettima mai suna, TinKas Tinubu/Shettima Support Group.

Bola Ahmed Tinubu.
Wani Bawan Allah Ya Taso Daga Gombe Zuwa Abuja Saboda Goyon Bayan Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Twitter

Jim kaɗan kafin fara wannan tattaki a Gombe, Umar ya shaida wa hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) cewa ya kudiri aniyar wannan tafiya ne domin nuna goyon bayansa ga Tinubu gabanin babban zaben 2023.

Kara karanta wannan

2023: Babban Dalilin da Yasa Na Ɓoye Manufofina Ga Yan Najeriya, Kwankwaso Ya Magantu

Yace kungiyarsu ta jima tana jawo hankalin mutane a yankin arewa maso gabas domin su mara wa APC baya kuma su tabbatar da nasarar yan takarar jam'iyyar a dukkanin matakai a zaɓe mai zuwa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mutumin yace:

"Tinubu ya zaɓi namu, Sanata Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa, babban abinda zamu saka masa da shi mu haɗa masa goyon baya da nufin tara musu tulin kuri'u daga yankin kudu maso gabas."
"Tinubu ya nuna zai iya kuma yana da kwarewa, haka Shettima saboda haka mara musu baya da tabbatar da sun yi nasara a zaɓen 2023 zai amfani yan Najeriya."
"Zan tafi Abuja a karan kaina domin na gayyaci jagororinmu Sanata Tinubu da Shettima da su zo nan su buɗe Ofishinmu na Kamfe a jihar Gombe."

Wane shiri Umar ya yi wa tafiyar?

Kara karanta wannan

2023: Saura Kiris Na Zama Shugaban Kasa, Bola Tinubu Ya Gana da Malaman Tijjaniyya a Kano

Jaridar Vanguard ta rahoto Mutumin mai 'ya'ya uku yace ya shirya wa wannan tafiya, inda ya ƙara da cewa:

"Na yi guzurin magungunan zazzaɓin cizon sauro ko da zan kwanta rashin lafiya a hanyar zuwa Abuja. Zan riƙa tafiya ne da rana idan dare ya yi zan nemi shingen jami'an tsaro na gabatar musu da kaina na kwana anan."
"Iyalaina sun goyi bayan abinda na kudiri aniya kuma suna tare da ni ɗari bisa ɗari da addu'o'insu."

A wani labarin kuma Gwamna Obaseki Yace mabiyan Peter Obi da za su kai labari ba, nan gaba kaɗan za'a nemi wannan tururin da suke a rasa

Gwamnan Edo dake kudu maso kudancin Najeriya, Godwin Obaseki, ya kaddamar kwamitin kamfen PDP na jiharsa.

Da yake tsokaci, Obaseki yace mabiyan Peter Obi ba zasu kai labari ba, duk wannan tururin da suke mai gushewa ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel