INEC ta Fitar da Sunayen ‘Yan takara, Kotu tace Jam’iyyar APC ta Sake Shirya Zabe

INEC ta Fitar da Sunayen ‘Yan takara, Kotu tace Jam’iyyar APC ta Sake Shirya Zabe

  • Alkalin Babban kotun tarayya a Akure ya yanke hukunci a kan rikicin ‘yan takaran APC a Akoko
  • Victor Ategbole ya yi karar INEC da shugabannin jam’iyyar APC da ya sha kashi a zaben tsaida ‘dan takara
  • Alkali ya saurari karar Lauyan Ategbole, ya bada umarni a shirya wani zaben nan da kwanaki bakwai

Ondo - Babban kotun tarayya mai zama a garin Akure da ke jihar Ondo, ta umarci jam’iyyar APC mai mulki ta shirya wani sabon zaben tsaida gwani.

Premium Times tace hukuncin da Alkali ya yi ya shafi takarar kujerar ‘dan majalisar tarayya na mazabar Akoko a Ondo a zaben da za ayi a shekarar 2023.

A sanadiyyar karar da Victor Ategbole ya shigar, za a sake shirya zaben 'dan takaran mazabar Akoko ta Kudu maso gabas da Akoko ta Kudu maso yamma.

Jam’iyyar APC za ta sanar da hukumar zabe na INEC wannan hukunci da aka yi domin a shirya sabon zaben tsaida ‘dan takara nan da kwanaki bakwai.

Dr. Victor Ategbole ya fara nasara a kotu

Dr. Victor Ategbole yana cikin wadanda suka nemi tikitin APC domin ya wakilci Akoko ta Kudu maso gabas/Akoko ta Kudu maso yamma a majalisa a 2023.

‘Dan siyasar ya kai korafi gaban Alkali yana neman a ruguza zaben fitar da gwanin da aka shirya wanda Asiwaju Adegboyega Adefarati ya yi galaba a kan sa.

Taron APC
Mata a taron APC Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Rahoton da muka samu daga Punch yace Ategbole yayi korafin cewa APC ba ta gudanar da zaben tsaida ‘dan takara a wurin da ta tsara tun farko ba.

Lauyan da ya tsayawa mai neman takaran yace jam’iyyar APC ta shirya zaben fitar da gwanin a garin Akure, ma’ana an fita daga mazabar Akoko gaba daya.

Alkali ya karbi koken mai kara

Blueprint tace Mai shari’a Demi Ajayi ya karbi korafin wanda ya shigar da kara, a karshe ya umarci INEC ta sake shirya wani zaben nan da mako guda.

Da wannan hukunci, ana sa ran shugabannin APC za su gudanar da wani sabon zabe a makarantar St. Patrick Secondary da ke Iwaro-Oka a garin na Akoko.

Wadanda suka kare kansu a wannan shari’a da aka yi sun hada da INEC, shugaban APC na kasa, da Hon. Ade Adetimehin wanda ke rike da jam’iyya a jihar.

Takarar Atiku ta kara karfi

An ji labari Goodluck Jonathan ya hango wanda zai yi nasara, ya yi sabon hasashe a kan 2023 a lokacin da ya gana da Gwamna Ifeanyi Okowa a ranar Alhamis.

Jonathan ya tsaida matsaya, ya bayyana cewa Atiku Abubakar da Ifeanyi Okowa na jam'iyyar PDP ne ‘yan takararsa a zaben Shugaban kasa da za ayi a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel