Shugaban Matasan Arewa Da Ya Taka Rawar Gani Don Nasarar Buhari A 2015 Ya Fita Daga APC Ya Koma Labour Party

Shugaban Matasan Arewa Da Ya Taka Rawar Gani Don Nasarar Buhari A 2015 Ya Fita Daga APC Ya Koma Labour Party

  • Tsohon shugaban matasan arewa, Isaac Balami ya fita daga jam'iyyar APC mai mulki ya koma Labour Party
  • Da ya ke magana a matakin da ya dauka, Balami ya ce a wannan matakin mai muhimmanci a kasar, APC ba zabi bane
  • Dan siyasan haifafan jihar Borno kuma tsohon shugaban matasan APC ya kuma sayar da jiragen samansa

FCT Abuja - Fitaccen shugaban matasan Najeriya kuma kwararre a bangaren sufurin jiragen sama, Kwamared Isaac Balami ya fita daga jam'iyyar APC ya koma Labour Party, LP, rahoton Nigerian Tribune.

Balami wanda ya taka muhimmin rawa wurin nasarar Shugaba Muhammadu Buhari a 2015 lokacin da ya tattaro kan matasan yankin, ya bayyana hakan ne a wani sanarwa mai taken "My Critical Junction."

Kara karanta wannan

Musulmi da Musulmi: Tsohon Sakataren Buhari Ya Fallasa Wasu Kulle-Kullen da Tinubu Ke Yi Gabanin 2023

Balami Isaac
2023: Tsohon Shugaban Matasan Arewa Ya Fita Daga APC, Ya Sayar Da Jiragen Samansa, Ya Koma Labour Party. Hoto: @balamiisaac.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tsohon kakakin kungiyar matukan jiragen sama da injiniyoyi ya ce ya fita daga APC ne ya koma LP saboda yana cikin yan Najeriya, musamman kiristoci ba da ba su ji dadin rashin adalci da aka musu a APC ba.

Tsohon shugaban na 7STAR Hangar/Airlines ya yi magana kan tikitin musulmi da musulmi na APC matsayin daya cikin babban dalilinsa na fita daga jam'iyyar.

Wani sashi na jawabinsa:

"Idan aka duba baya, musulmin arewa cikin shekaru 24 sun mori manyan mukamai biyu na shugaban kasa ko mataimaki, da hadin kan kiristocin arewa.
"Don haka, bai dace ba lokacin da dama ta samu da za a bawa kiristocin arewa dama a matsayin abokin takara a APC, sai aka yi watsi da shi."

Da ya magana kan dalilin da yasa matakinsa ke da muhimmanci a yanzu, ya ce:

Kara karanta wannan

Dailin Da Yasa Na Yi Shiru Game da Rikicin Atiku da Gwamna Wike, Saraki Ya Magantu

"Amma akwai lokaci, mai muhimmanci, a rayuwa da dole za a dauki matakai masu tsauri. Wannan shine lokacin da mutum zai zabi abin da ya ke dai-dai duk wahalarsa.
"A matsayi na na matashi, da ke jagoranci tsakanin tsara na kuma daya cikin masu aiki a bangaren da aka fi girmamawa a Najeriya, a yau na nuna cewa ya yi ammana da yin adalci da aka kafa rayuwarmu a kai."

'Karyar Peter Obi Ta Wadatar Da Afirka Baki Daya', Jigon PDP Ya Ragargaji Dan Takarar Shugaban Kasa Na LP

A wani rahoto, hadimin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Reno Omokri ta ce dan takarar shuganan kasa na Labour Party, LP, Peter Obi ya rasa kuri'un yarbawa saboda yi wa Asiwaju Bola Tinubu, dan takarar APC izgili.

Omokri, ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi, 11 ga watan Satumba ta shafinsa na Twitter kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel