'Karyar Peter Obi Ta Wadatar Da Afirka Baki Daya', Jigon PDP Ya Ragargaji Dan Takarar Shugaban Kasa Na LP

'Karyar Peter Obi Ta Wadatar Da Afirka Baki Daya', Jigon PDP Ya Ragargaji Dan Takarar Shugaban Kasa Na LP

  • Da farko, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party ya ragargaji magoya bayan Asiwaju Bola Tinubu a wani bidiyo da ke yawo a intanet
  • Tsohon gwamnan na Anambra ya ce dan takarar na APC ba shi da lafiya yana mai cewa masu goyon bayansa kawai kudinsa suke so
  • Amma, hakan bai yi wa Reno Omokri dadi ba wanda a martaninsa ya soki maganar da Obi ya yi yana mai cewa ya rasa kuri'un yarbawa saboda yi wa Tinubu izgili

Hadimin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Reno Omokri ta ce dan takarar shuganan kasa na Labour Party, LP, Peter Obi ya rasa kuri'un yarbawa saboda yi wa Asiwaju Bola Tinubu, dan takarar APC izgili.

Omokri, ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi, 11 ga watan Satumba ta shafinsa na Twitter kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

APC Ta Yi Magana Kan Lafiyar Bola Tinubu da Yiwuwar Janye Takarar Shugaban Kasa

Tinubu II
'Karyar Peter Obi Ta Wadatar Da Afirka Baki Daya', Jigon PDP Ya Ragargaji Dan Takarar Shugaban Kasa Na LP. Hoto: @OfficialBAT.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mai rajin kare hakkin bil adaman ya ce:

"Peter Obi ya rasa dukkan kuri'un Yarbawa! Duba yadda ya yi wa shugabanin yarbawa karya. Yana raina Tinubu. Yana izgili kan lafiyarsa da dukiyarsa. Yana magana tamkar Nnamdi Kanu. Wannan shine Peter Obi na ainihi da muka gani. Wanda muke gani a baya Peter Obi na bogi ne! #TableShaker."

A cewar Omokri, Obi ya wakilci Najeriya a gasar karya yayin wasannin Olympics mai zuwa don tabbatar da cewa Najeriya ta lashe gwal.

Ya jadada hakan da cewa:

"Zai iya wakiltar Afirka wurin karya. Ta yaya shugabannin yarbawa za su ce kada yarbawa su zabi Peter saboda zai gina tashohin ruwa a kudu maso kudu, alhalin kudu maso kudu na da isasun tashohin jirgin ruwa? #TableShaker."

Tinubu ba haka ya ke harkokinsa ba, IPOB ne suka rubuta irin wannan sakon, a cewar Omokri

Kara karanta wannan

Ta Yaudareshi Bayan Kashe Mata N150,000 Ta Auri Wani: Mutumin Yola Ya Bankawa Amarya Da Ango Wuta

Omokri ya kara da cewa:

"Bana tsammanin rubutun da @PeterObi ya yi ikirarin ya fito daga @OfficialBAT daga Tinubu ya fito. Na san yan IPOB da ke goyon bayan Peter sun kware wurin rubuta irin wannan sakonnin su fitar da su, suna ikirarin daga Atiku da Tinubu ne. Sun taba min hakan."

Martanin wasu yan Najeriya

Yan Najeriya sun bayyana ra'ayoyinsu kan lamarin a shafin Facebook na Legit.ng

Kaman Yilchini

"Ina zaton ya yi wa yarbawa izgili ne amma tunda Tinubu ne kadai, Reno ya matar da hankali kan Atiku..
"Mun san Reno baya kaunar Obi."

Imo Emereole Ogbonnaya ya ce:

"Ya zo Najeriya ya fada mana wannan.
"Reno yana jin dadin mulkin shugabanni na gari amma yana son mu cigaba da shan wahala."

Nwahandi Queen ta ce:

"Reno kawai yana son kirkirar kiyayya ne ga Obi kuma ba zai yi nasara ba."

Adebisi Ademighty shi kuma cewa ya yi:

Kara karanta wannan

A Sauya Sunan Aso Rock Ko Sauran Yankunan Arewa Zuwa Sunan Sarauniya Elizabeth, Ohanaeze Ga FG

"Obi da ba zai iya kayar da atiku a zaben fidda gwanin PDP ba yana son ya kayar da Tinubu."

Ka Ja Kunnen Magoya Bayan Ka, Tinubu Ya Gargadi Peter Obi Kan Yada Labaran Karya

A wani rahoton, Asiwaju Bola Tinubu, ya bukaci takwararsa na Labour Party, Mr Peter Obi, ya ja kunnen magoya bayansa don su dena yada karya, makirci da aibanta shi da sauran yan takara.

Tinubu, cikin sanarwar da direktan watsa labaransa, Mr Bayo Onanuga ya fitar, ya bukaci Obi ya ja kunnen magoya bayansa kuma ya bari zaben 2023 ya zama kan batutuwan da za su bunkasa kasa, cigaba da kwanciyar hankalin Najeriya, yana gargadin "karya da yada maganganu marasa tushe za ba su saka a ci zabe ba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel