An Sanar Da Wanda Ya Lashe Zaben Dan Takarar Gwamnan PDP A Zamfara

An Sanar Da Wanda Ya Lashe Zaben Dan Takarar Gwamnan PDP A Zamfara

  • Dr Dauda Lawal Dare ya sake lashe zaben fidda gwani na gwamna a karkashin jam'iyar PDP a Jihar Zamfara
  • Hassan Hyet, shugaban kwamitin zaben ya ce Dauda ya samu kuri'u 422, masu biye da shi Ibrahim Shehu da Hafiz Mohmmed suka samu kuri'u daya kowannensu
  • Tunda farko, Ibrahim Shehu ne da wasu yan takarar suka kai kara kotu har ta kai ga Alkali ya bada umurnin sake yin zaben

Zamfara - Dr Dauda Lawal-Dare ya sake zama dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP a jihar Zamfara a zaben fidda gwani da aka kammala gabanin babban zaben 2023, Channels TV ta rahoto.

Dauda Lawal-Dare ya samu kuri'u 422 inda ya lashe zaben a jihar ta arewa maso yamma yayin da Ibrahim Shehu da Hafiz Mohammed suka samu kuri'a daya kowannensu. Wani dan takarar, Wadatau Madawaki, bai samu ko kuri'a daya ba a zaben na ranar Juma'a.

Dr Dauda
An Sanar Da Wanda Ya Lashe Zaben Dan Takarar Gwamnan PDP A Zamfara.Hoto: @ChannelsTV.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Shugaban kwamitin zaben, Hassan Hyet, ya sanar da Dauda Lawal-Dare a matsayin wanda ya lashe zaben saboda samun kuri'u mafi yawa kuma an fatan zai sake dawowa a matsayin dan takarar gwamna na jam'iyyar a zaben 2023.

Ya ce:

"Bisa dokokin zaben da jam'iyya, ina son sanar da cewa Dr Dauda Lawal Dare shine halastaccen zababen dan takarar gwamnan PDP na jihar Zamfara a zaben 2023."

Hassan, wanda aka tura shi Zamfara daga Abuja domin ya gudanar da zaben ya ce an kada kuri'u cikin zaman lafiya da lumana da adalci.

Kuri'un da yan takarar suka samu a zaben na PDP a Zamfara

A zaben raba gardamar, daliget fiye da 455 suka shiga zaben, amma 431 aka tantance, jimillar kuri'un da aka kada shine 428.

An yi zaben raba gardamar na ranar Juma'a ne bayan hukuncin babban kotun tarayya na Abuja da ta soke zabe da aka yi na baya inda Dauda ya yi nasara.

Kotun ta yi hukuncin ne sakamakon kara da Ibrahim Shehu da wasu yan takara biyu suka shigar.

Mai shari'a Aminu Bappa na babban kotun tarayya ne a Gusau ya soke zaben fidda gwanin na farko da Dauda ya yi nasara, ya bada umurnin sake sabuwar zabe.

Dakaci karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Online view pixel