Jam'iyyar PDP Ta Sanya Ranar Canza Zaben Fidda Ɗan Takarar Gwamnan Zamfara

Jam'iyyar PDP Ta Sanya Ranar Canza Zaben Fidda Ɗan Takarar Gwamnan Zamfara

  • Jam'iyyar PDP tace zata gudanar da sabon zaɓen fidda ɗan takarar gwamnan Zamfara a 2023 bayan Kotu ta soke na baya
  • Shugaban PDP a jihar, Sani Ƙaura, yace shirye shirye sun yi nisa domin bin umarnin Kotu gobe Jumu'a 23 ga watan Satumba
  • A ranar Jumu'a ta makon da ya gabata ne Kotun tarayya dake Gusau ta soke zaɓen bisa hujjar karya dokoki

Zamfara - Jam'iyyar PDP ta zaɓi ranar Jumu'a (Gobe) domin sake sabon zaɓen fidda gwani na takarar gwamnan jihar Zamfara a zaɓen 2023, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A makon da ya gabata ne, babbar Kotun tarayya dake zama a Gusau ta soke zaɓen fidda gwanin wanda Alhaji Dauda Lawal Dare, ya yi nasara bisa hujjar yi wa tanadin kundin jam'iyyar hawan kawara.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamna Tambuwal ya karbe mukamin shugaban gwamnonin Najeriya

Jam'iyyar PDP.
Jam'iyyar PDP Ta Sanya Ranar Canza Zaben Fidda Ɗan Takarar Gwamnan Zamfara Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Tun da farko, tsohon ɗan majalisar tarayya, Alhaji Ibrahim Shehu Gusau, ya roki Kotun ta soke zaben wanda a cewarsa zagaye yake da tulin saɓa wa doka.

Shugaban PDP a jihar Zamfara, Alhaji Ahmad Sani Ƙaura, yace shirye-shirye sun kankama domin ganin an gudanar da zaɓen lami lafiya, inda ya ƙara da cewa za'a ba kowane ɗan takara dama ya taka wasansa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Su waye ke neman takara a PDP?

"PDP jam'iyya ce mai bin doka kuma zamu cika umarnin Kotu na shirya sabon zaben fidda gwani, masu neman takara suna nan yadda suke, Alhaji Dauda Lawal Dare, Ibrahim Shehu Gusau, Wadatau Madawaki da Hafiz Nahuche."
"Uwar jam'iyya ta ƙasa ta tsara gudanar da zaɓen ranar 23 ga watan Satumba, 2022 (Gobe). Jami'ai zasu zo Gusau daga hedkwata domin sa ido wajen gudanar da sahihi kuma amintaccen zaɓe."

Kara karanta wannan

2023: Dole Mu Tabbatar da Najeriya Gabanin Shugaban Kasa, Jonathan

"Yanzu da nake magana da ku ana gudanar da taruka a matakin gundumomi saboda daga cikin hukuncin Kotu tace an nuna wa mata wariya a Deleget."

- Sani Ƙaura.

A wani labarin kuma Bayan Su Wike, Wasu Kusoshin Siyasa a Tafiyar Atiku Sun Goyi Bayan Tinubu a 2023

Jam'iyyar PDM, wacce marigayi Shehu Musa Yar'adua ya kafa daga baya ta koma tafiyar siyasar Atiku, ta yi watsi da tsohon mataimakin shugaban.

Jam'iyyar wacce aka rushe ta ayyana goyon bayanta ga Tinubu na APC tare da wasu ƙungiyoyi, sun ce shi ya fi dacewa da shugabanci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel