Jam’iyyar PDP a Zamfara Ta Fara Shirye-Shiryen Sake Zaben Fidda Gwanin Gwamna

Jam’iyyar PDP a Zamfara Ta Fara Shirye-Shiryen Sake Zaben Fidda Gwanin Gwamna

  • Jam'iyyar PDP a jihar Zamfara za ta sake zaben fidda gwani, kuma tuni aka fara tantance 'yan takara
  • Kotu ta umarci jam'iyyar ta PDP da ta tabbatar da sake zaben fidda gwanin dan takarar gwamna a jihar Zamfara
  • A baya jam'iyyar PDP ta ce za ta duba yiwuwar daukaka kara, amma ta ce babu lokacin yin hakan a yanzu

Jihar Zamfara - Jam'iyyar PDP a jihar Zamfara ta fara gudanar sabon zaben fidda gwanin gwamna gabanin babban zaben 2023 mai zuwa badi, Channels Tv ta ruwaito.

Wannan na zuwa ne jim kadan bayan da babbar kotun tarayya ta rusa zaben fidda gwanin da aka gudanar a watannin baya, wanda ya samar da Dauda Lawan a matsayin dan takarar gwamna.

Hukuncin kotun ya samo asali ne daga karar Ibrahim Shehu da wasu 'yan takara biyu na jam'iyyar suka shigar, inda suka kalubalanci sakamakon zaben.

PDP ta fara gudanar da sabon zaben fidda gwani a Zamfara
Jam’iyyar PDP a Zamfara Ta Fara Shirye-Shiryen Sake Zaben Fidda Gwanin Gwamna | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Hukuncin da mai sharia Aminu Bappa na kotun tarayya ya yanke a Gusau a makon jiya ya rusa zaben, kuma ya ba da umarnin sake zaben fidda gwanin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dalilin da yasa za a sake zaben fidda gwani

Sakataren jam'yyar PDP a jihar Zamfara, Alhaji Ahmad Farouq Rijiya ya bayyana cewa, za a sake zaben fidda gwanin ne saboda karancin lokaci da jam'iyyar ke dashi na daukaka kara.

A bangare guda, ya kirayi 'yan takarar jam'iyyar da su mai da hankali tare da bin doka da oda kamar yadda kundin tsarin jam'iyyar ya tanada, rahoton Daily Post.

Daga karshe ya ce, jam'iyyar PDP ta bi doka ta hanyar bin umarnin kotu, don haka ya kamata 'yan takara su zama masu taka rawar gani wajen tabbatar kaucewa matsala a zaben da za a yi.

Jam'iyyar PDP Ba Ta Dan Takaran Gwamna a Zaben 2023, Kotu Ta Soke Zaben Fidda Gwani

A makon da ya gabata, wata babbar kotun tarayya dake Gusau, jihar Zamfara, ta soke zaben Dauda Lawal a matsayin dan takaran gwamnan jihar na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Lawal ya lashe zaben fidda gwanin jam'iyyar ne a ranar 25 ga watan Mayu, 2022.

Wasu yan takarar uku, — Abubakar Nakwada, Wadatau Madawaki, and Ibrahim Shehu-Gusau — sun janye daga zaben saboda zargin magudi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel