Gwamnoni ne Babbar Barazana ga Damokaradiyyar Najeriya, Ghali Na'Abba

Gwamnoni ne Babbar Barazana ga Damokaradiyyar Najeriya, Ghali Na'Abba

  • Ghali Umar Na'abba, tsohon kakakin majalisar wakilai, ya koka kan yadda gwamnoni ke kokarin murkushe damoradiyya a Najeriya
  • Na'abba ya bayyana cewa, yanzu gwamnoni ke nada 'yan takara, babu batun yin zabukan fidda gwani a jihohin kasar nan
  • Yace hakan babban nakasa ce ga damoradiyya kuma babu shakka shi ke haifar da shugabannin da basu cancanta ba

Kano - Tsohon kakakin majalisar wakilan Najeriya, Alhaji Ghali Umar Na'Abba, yace gwamnonin jihohi a Najeriya sune babbar barazana ga damokaradiyyar kasar nan.

Kamar yadda Daily Trust ta rahoto, Na'abba yace gwamnoni sun killace jam'iyyun siyasa kuma su ke yanke hukuncin wanda zai nemi takarar kujerun siyasa wanda hakan ke gurgunta damokaradiyya kuma a cigaba da juya mulki tsakaninsu ba tare da duba cancanta ba.

Ghali Umar Na'abba
Gwamnoni ne Babbar Barazana ga Damokaradiyyar Najeriya, Ghali Na'Abba. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Na'abba wanda ke wannan jawabi a gidansa dake Kano yayin da ya karba wakilan Kungiyar Matasan Na'abba a wata ziyara, yace 'yan kasa yanzu gudun siyasa suke yi saboda abinda gwamnoni suke yi yanzu.

Kara karanta wannan

Gwamna Soludo ya Wanke Fulani, Ya Bayyana Wadanda ke Assasa Rashin Tsaro a Anambra

Yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Tun 1999 gwamnoni ke da matsala a kasar nan. Sun bada gudumawa wurin mutuwar damkokaradiyya a cikin jam'iyyun siyasa.
"Kuma idan ba a yi zabuka a cikin jam'iyyu ba, toh za a iya samu bara-gurbin shugabanni da zasu lalata dukkan siyasar kasar.
"Gwamnonin ne suka janyo hakan. Da wuya ka ga an yi zaben fidda gwanin jam'iyyu. A maimakon hakan sai su ce a fitar 'dan takarar yarjejeniya wanda hakan bai dace ba."

Ya cigaba da cewa:

"Idan muna son ganin canji a kasar nan da gaske, dole ne mu canza damorakadiyyarmu kuma mu bai wa kowa dama.
"Mu bada damar zabe a cikin jam'iyyu ta yadda talakawa da masu kudi zasu samu rawar takawa. Wannan ne kadai zai iya kawo canji ba abinda gwamnoni ke yi ba.
"Babu inda hakan zai kai mu, a maimako ma sai dai ya lalata halin da kasar ke ciki."

Kara karanta wannan

2023: Tsohon Kakakin Majalisar Tarayya, Ghali Na'Abba, Ya Sauya Sheka Zuwa PDP, Ya Fallasa Sirrin APC

Falana Yayi wa FPRO Martani, Yace Shekaru 25 a Gidan Maza ne Hukunci 'Dan Sandan Da ya Mari Farar Hula

A wani labari na daban, lauya mai rajin kare hakkin 'dan Adam kuma Babban Lauyan Najeriya, Femi Falana, ya caccaki mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Najeriya, Olumuyiwa Adejobi kan tsokacinsa na yadda 'yan Najeriya ya dace su yi martani idan 'yan sanda sun ci zarafinsu.

Adejobe ya janyo cece-kuce a ranar Asabar yayin da yace 'yan Najeriya basu da damar yin martani inda 'yan sanda sun ci zarafinsu, Channels TV ta rahoto.

Yace a kodayaushe 'yan sanda suna da kariya kan wani farmaki da za a kawo musu a shari'ance.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng