Falana Yayi wa FPRO Martani, Yace Shekaru 25 a Gidan Maza ne Hukunci 'Dan Sandan Da ya Mari Farar Hula

Falana Yayi wa FPRO Martani, Yace Shekaru 25 a Gidan Maza ne Hukunci 'Dan Sandan Da ya Mari Farar Hula

  • Babban lauya mai rajin kare hakkin 'dan Adam, Femi Falana, ya caccaki mai magana da yawun 'yan sandan Najeriya kan batun marin farar hula
  • Falana yace hukuncin shekaru 25 ne kan 'dan sandan da ya mari farar hula, amma shekaru 3 kan farar hula idan ya mari 'dan sanda
  • Kamar yadda yace, dokokin kasa sun haramtawa 'dan sanda, duka, zagi, cin zarafi ko azabtar da farar hula, kuma an bukaci farar hula su mutunta 'yan sanda

Lauya mai rajin kare hakkin 'dan Adam kuma Babban Lauyan Najeriya, Femi Falana, ya caccaki mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Najeriya, Olumuyiwa Adejobi kan tsokacinsa na yadda 'yan Najeriya ya dace su yi martani idan 'yan sanda sun ci zarafinsu.

Kara karanta wannan

Mabaraci Ya Tsallake Rijiya Da Baya Yayinda Aka Kamashi Kudi N500,000 a jihar Legas

Adejobe ya janyo cece-kuce a ranar Asabar yayin da yace 'yan Najeriya basu da damar yin martani inda 'yan sanda sun ci zarafinsu, Channels TV ta rahoto.

Yace a kodayaushe 'yan sanda suna da kariya kan wani farmaki da za a kawo musu a shari'ance.

Femi Falana
Falana Yayi wa FPRO Martani, Yace Shekaru 25 a Gidan Maza ne Hukunci 'Dan Sandan Da ya Mari Farar Hula. Hoto daga channelstv.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Idan 'dan sanda sanye da kayan aiki ya zabgawa farar hula mari, farar hula bashi da damar ramawa. Bayan haka, idan yana sanye da kayan aiki, rashin mutunta Najeriya ne ka doki 'dan sanda da kaya a jikinsa.
"Wannan rashin mutuntawar ba 'dan sanda kayi wa ba, kasar ce kayi wa kuma laifi ne dake kunshe a dokokin laifukan kasa."

- Yace.

Amma a yayin martani kan batun, Falana yace duk wani cin zarafi kan 'dan Najeriya na iya janyowa mutum zaman shekaru 25 a gidan yari kamar yadda yake kunshe a hakkokin 'dan kasa.

Kara karanta wannan

An Kama Mutune 5 Kan Kisar Dan Sanata Kabiru Gaya Mai Wakiltar Kano, An Samu Karin Haske Kan Dalilin Kisarsa

A yayin bayyana dokokin laifuka da hukuncinsu na 2015 da kuma na 'yan sanda na 2020, Falana yace an haramtawa 'yan sanda da sauran jami'ai cin zarafi, cin mutunci ko tozarta 'dan Najeriya har da masu laifi.

"Amma dogaro da sashi na 34 na kundin tsarin mulkin Najeriya, kowanne 'dan kasa yana da hakkin mutuntawa daga wani. Har ila yau, babu 'dan kasar da za a iya cin ma zarafi, a bayyane ko kuma a zabtar da shi."

- Falana yace.

"An bukaci farar hula da su mutunta 'yan sanda dake bakinaikinsu na tabbatar da doka. Hukuncin mari ko cin zarafin jami'in 'dan sanda shekaru 3 ne a gidan yari karkashin Criminal Code. Har ila yau. ana tabbatar da cewa dole ne 'yan sanda su mutunta farar hula."

- Falana ya kara da cewa.

Hukumar 'Yan Sanda: Idan Dan Sanda Ya Kafta Maka Mari, Ya Daki Banza Matukar Yana Sanye Da Inifam

Kara karanta wannan

Yadda Jikan Sarauniya Elizabeth II Ya Gaji Tamfatsetsen Gidanta Mai Darajar N426b

A wani labari na daban, kakakin rundunar yan sandan Najeriya, Olumuyiwa Adejobi, ya bayyana cewa idan da jami’in dan sanda zai mari wani dan farin hula, mai shi bai da damar ramawa.

Adejobi, wanda ya je shafinsa na Twitter don bayyana hakan, ya shawarci duk wanda irin haka ta cika da shi da ya shigar da kara a gaban hukumar doka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel