2023: Ɗan Takarar Gwamna a PDP Ya Roki Tsohon Sakataren Gwamnati Ya Fice APC

2023: Ɗan Takarar Gwamna a PDP Ya Roki Tsohon Sakataren Gwamnati Ya Fice APC

  • Jam'iyyar PDP a jihar Katsina ta fara zawarcin tsohon Sakataren gwamnatin Jiha, Dakta Mustapha Inuwa
  • Ɗan takarar gwamna a inuwar PDP, Sanata Lado Ɗanmarke, ya ziyarci Inuwa tare da rokon ya yafe abinda PDP ta masa a baya
  • Mustapha Inuwa, wanda ya rasa tikitin takarar gwamna a zaɓen fidda gwanin APC, yace zai tattauna da magoya bayansa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Katsina - Yayin da ake tunkarar babban zaɓen 2023, ɗan takarar gwamnan Katsina a inuwar PDP, Sanata Yakubu Lado Ɗanmarke, ya ziyarci tsohon Sakataren gwamnatin jiha, Mustapha Inuwa.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa yayin wannan ziyara, Lado Ɗanmarke, ya roki tsohon SSG ya sauya sheka zuwa PDP domin su haɗa ƙarfi su tunkari 2023.

Mustapha Inuwa, wanda ya rasa tikitin APC ta hannun tsohon shugaban hukumar SEMDAN, Dr Diko Raɗɗa, ya karɓi baƙuncin Lado da tawgarsa a Ofishinsa na Kamfe dake cikin birnin Katsina.

Kara karanta wannan

Jigon Jam'iyyar PDP Kuma Shugaban Wata Hukuma Ya Mutu Bayan Ya Yanke Jiki Ya Faɗi

Lado da Mustapha Inuwa.
2023: Ɗan Takarar Gwamna a PDP Ya Roki Tsohon Sakataren Gwamnati Ya Fice APC Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa tsohon Sakataren bai ji daɗin yadda zaɓen fidda gwanin APC ya gudana ba kuma ya tsame kansa daga harkokin jam'iyyar tun lokacin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yayin da yake jawabi da tsohon Sakataren da tawagar magoya bayansa, Yakubu Lado, yace:

"Mun zo nan ne domin mu roki yayanmu (Mustapha Inuwa), ginshiƙin siyasa wanda ya bar PDP a baya kan wasu dalilai, muna rokon ya dawo gida mu haɗa karfi a kokarin mu na ceto Najeriya."
"Muna masu ba shi hakuri kuma muna rokon ya manta da duk rashin adalcin da PDP ta masa a baya. Mun san karfinsa kuma mun san abinda zai iya yi, saboda haka muna roko tare da fatan ya dawo PDP mu haɗa kai wajen ceto ƙasa."
"Tare da goyon bayansa, kwarin guiwar mu zai ƙaru kan cewa da ikon Allah jam'iyyar PDP zata lashe zaɓe a jihar Katsina tun daga sama har ƙasa."

Kara karanta wannan

2023: Hanya Ɗaya Da Zamu Kawo Karshen Rikicin Jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar Ya Magantu

Shin ya amince da komawa PDP?

Da yake martani, Dakta Mustapha Inuwa, ya gode wa Lado da 'yan tawagarsa bisa wannan ziyara, inda ya yi bayanin cewa babu aboki ko ɗan adawa na har abada a siyasa, kowa da ra'ayinsa.

Inuwa ya jaddada bukatar 'yan Najeriya su zaɓi shugabanni nagari da zasu gyara ba daidai ba a cikin al'umma. Ya tabbatar wa wakilan PDP cewa zai duba buƙatarsu kamin ya yanke hukunci tare da masoyansa.

Legit.ng Hausa ta nemi jin ta bakin wani jigon APC kuma makusancin ɗan majalisar jiha mai wakiltar Ɗanja, Shamsudden Chiroma, yace tun bayan cin zaɓen 2015 APC ta tafka kuskure.

Ɗan siyasan wanda ya nemi a sakaya sunansa yace a ra'ayinsa duk abinda Mustapha Inuwa, ya yi bai laifi ba ko da kuwa ya koma PDP.

"Mustapha Inuwa ya taimaki gwamna Masari ya ci zaɓe sau biyu, amma da yake neman takara Masari bai taimake shi ba, banga laifinsa ba. Haka a matakin ƙasa, waɗan da suka taimaki Buhari ba su ya jawo a jiki ba."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamna Aminu Tambuwal Ya Yi Murabus Daga Kan Muƙaminsa Na PDP

Bugu da ƙari, a kalamansa ya gargaɗi masu ruwa da tsaki na APC a jihar Katsina su tashi tsaye, idan ba haka ba kuma sakamkon zaɓen 2023 ya barsu baki buɗe.

A wani labarin kuma Bayan Tinubu, Wani Gwamnan APC Ya Faɗi Wanda Yake Kaunar Ya Gaji Buhari a 2023

Gwamnan Ebonyi, Dave Umahi, yace tafiyar Peter Obi ta ƙara nuni da cewa Kudu maso gabas ba abin jefarwa bane a harkokin siyasar Najeriya.

Jim kaɗan bayan gana wa da Buhari a Abuja, Umahi yace idan aka ɗauke Tinubu, to zai so Peter Obi na ɗare kujerar shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel