Bayan Tinubu, Gwamnan APC Ya Fadi Dan Takarar Da Zai Zaba Magajin Buhari a 2023

Bayan Tinubu, Gwamnan APC Ya Fadi Dan Takarar Da Zai Zaba Magajin Buhari a 2023

  • Gwamnan Ebonyi, Dave Umahi, yace tafiyar Peter Obi ta ƙara nuni da cewa Kudu maso gabas ba abin jefarwa bane a harkokin siyasar Najeriya
  • Jim kaɗan bayan gana wa da Buhari a Abuja, Umahi yace idan aka ɗauke Tinubu, to zai so Peter Obi na ɗare kujerar shugaban kasa
  • Sai dai a cewarsa Jam'iyyar APC ce zata samu nasara amma Obi zai kwamushi kuri'u da yawa a yankin

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, yace a matsayinsa na ɗan APC zai mara wa jam'iyyarsa baya ta lashe zaɓe amma idan Allah ya yi nashi ikon, to yana da ɗan takara.

Jatridar Punch ta ruwaito gwamnan na cewa idan har aka cire jam'iyyar APC da ɗan takararta, to mutumin da zai zaɓa domin ya ɗare kujerar shugaban ƙasa shi ne Peter Obi na jam'iyyar LP.

Kara karanta wannan

2023: Gwamna Ya Gana da Tsohon Shugaban Kasa, Ya Faɗi Yadda Zasu Kifad Da Atiku a Arewa

Shugaba Buhari tare da gwamna Umahi.
Bayan Tinubu, Gwamnan APC Ya Fadi Dan Takarar Da Zai Zaba Magajin Buhari a 2023 Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Umahi, wanda ya gwabza da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a zaɓen fidda gwani na tikitin shugaban ƙasa, ya ayyana kansa da cikakken ɗan APC biyayya dake fafutukar nasarar APC a zaɓe.

Gwamnan ya yi wannan jawabin ne yayin zantawa da manema labaran gidan gwamnati jim kaɗam bayan gana wa da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, a Aso Rock, Abuja.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da yake amsa tambayoyin yan jarida, Umahi ya ayyana tafiyar Obi da buɗe ido da wayar da kai dake nuni da cewa yankin kudu maso gabas ba kanwar lasa bace a harkokin siyasar Najeriya.

Ko takarar Obi na da alaƙa da raguwar kashe-kashe a yankin?

"Ba zaka alaƙanta raguwar kashe-kashe a Kudu maso gabas da takarar Ibo ba, idan ka duba da kyau tsaro na ƙara samuwa a faɗin kasa baki ɗaya kuma ba shi da alaƙa da tafiyar Obi," Inji gwamnan.

Kara karanta wannan

2023: Hanya Ɗaya Da Zamu Kawo Karshen Rikicin Jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar Ya Magantu

Umahi ya jaddada cewa a matsayinsa na ɗan APC dole ya mara jam'iyyarsa baya ta samu nasara, "Amma idan Allah yace A'a, mutum na gaba a zaɓina shi ne Peter Obi saboda na yi imani da haka."

"Haka kuma zan faɗa a ko ina cewa a tsarin mulkin karɓa-karba tsakanin Kudu da arewa bayan ɗan arewa ya shafe shekara 8, babu wata kwaskwarima da za'ai har ɗan arewa ya sake neman wasu shekarun 8."

A wani labarin kuma kun ji cewa Tsoho Ministan Ya Fallasa Wani Sirri, Ya Faɗi Abu Ɗaya Da Zai Sa Yan Najeriya Su Zaɓi APC a 2023

Tsohon ministan wasanni a Najeriya kuma ɗan takarar Sanatan Kwara ta tsakiya yace ba ɗan Najeriyan da zai zaɓi APC a 2023.

Mallam Bolaji Abdullahi, mai neman sanata a inuwar PDP, ya ce wahalallu masu son cigaba da wahala ne zasu yi tunanin ƙara amince wa APC.

Kara karanta wannan

"Dole Ya Sauka" Gwamna Wike Ya Maida Zazzafan Martani Ga Majalisar Koli Ta PDP Kan Ayu

Asali: Legit.ng

Online view pixel