Daga Karshe, Bola Tinubu Ya Bayyana Yawan Shekarunsa Na Gaskiya

Daga Karshe, Bola Tinubu Ya Bayyana Yawan Shekarunsa Na Gaskiya

  • Ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana gaskiyar yawan shekarunsa a duniya
  • A ranar Laraba 31 ga watan Agusta, Tinubu ya sanar da cewa shekarunsa ɗaya da babban Malamin Katolika a Sakkwato, Matthew Hassan Kukah
  • Tsohon gwamnan jihar Legas ya ce akwai babban ruɗani kan halin da ƙasa ta tsinci kanta

A wurin bikin cika shekaru 70 a duniya na Malamin Kiristan nan, Matthew Hassan Kukah, na cocin Katola a jihar Sakkwato, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya yi tsokaci kan gaskiyar yawan shekarunsa.

Tinubu wanda ya yaba wa Kukah a wurin taron da ya samu halartar fitattun 'yan Najeriya, ya ce kamar wanda suka taru dominsa, shi ma shekarunsa 70 a duniya, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Daga Karshe, Bola Tinubu Ya Bayyana Yawan Shekarunsa Na Gaskiya Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Ɗan takarar kujerar shugaban ƙasa karƙashin inuwar jam'iyyar APC ya yaba wa Malamin wanda ya yi ƙaurin suna wajen bayyana ra'ayinsa bisa gina Ma'aikata, "The Kukah Project" domin ƙayata bikin karin shekararsa.

Kara karanta wannan

Rikici Ya Tsananta: Butulci da Girman Kai Ba Zasu Kaika Ko Ina Ba, Wike Ya Caccaki Shugaban PDP

Tinubu ya kara da cewa fiye da mafarkin Malamin da yake kokarin maida shi gaskiya, zai gina tubalin ɗaukakar Najeriya kuma wannan nauyi ne dake wuyan kowa, rahotonVanguard

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An shiga ruɗani a Najeriya - Tinubu

Kafin waɗan nan kalamai, Tinubu ya bayyana cewa ga dukkan alamu an shiga babban ruɗani game da halin da Najeriya ke ciki.

"Na saurari masu korafi, ya bayyana a zahiri mun shiga ruɗani game da halin da ƙasar nan ke ciki."

A wani labarin kuma Jerin Sunayen Jiga-Jigan PDP Na Ƙasa da Aka Gano Suna Rura Wutar Rikicin Atiku da Wike

Ana zargin tsoffin gwamnoni biyu daga jihohin Ondo da Kuros Riba da jagorantar rura wutar rikicin Atiku Abubakar da gwamna Wike.

Bayan su kuma ana zargin wasu tsofaffin Ministoci, wani Sanata da masu ruwa da tsaki a PDP da ƙara wutar rikicin Fetur.

Kara karanta wannan

Jigon APC Ya Fallasa Babban Abinda Tinubu Ke Tsoro Game Da Atiku, Kwankwaso a 2023

Asali: Legit.ng

Online view pixel