Yajin Aiki: An Huro Wa Shugaban ASUU Wuta Akan Kiran Wasu Jami'o'in Najeriya "Jabu"

Yajin Aiki: An Huro Wa Shugaban ASUU Wuta Akan Kiran Wasu Jami'o'in Najeriya "Jabu"

  • Shugaban kungiyar ASUU na kasa, Farfesa Emmanuel Osodoke ya yi wani magana da bai yi wa wasu jami'o'in Najeriya dadi ba
  • Shugaban na ASUU yayin hira da aka yi da shi kan yajin aiki ya ce duk jami'o'in jihohi da suka janye yajin aikin jami'o'in bogi ne
  • Wannan furucin ya janyo masa caccaka da suka daga wasu jami'o'in jihohin Najeriya inda suka bukaci ya janye maganan ya kuma basu hakuri

Farfesa Emmanuel Osodoke, shugaban kungiyar malaman jami'o'in Najeriya, ASUU, ya kira wasu jami'o'in jihohin Najeriya a matsayin makarantun 'bogi', The Cable ta rahoto.

Furta wannan kalmar ya janyo masa suka da daga wasu jami'o'in jihohin da kuma yan Najeriya a dandalin sada zumunta.

Osodoke
An Huro wa Shugaban ASUU Wuta Akan Kiran Wasu Jami'o'i Jabu. Hoto: @thecableng.
Asali: Twitter

Ya ce jami'un da su tare da ASUU a yajin aikin da ta ke yi ba mambobin su bane.

Kara karanta wannan

Yajin ASUU: Farfesa Maqari ya tona asirin malaman jami'a, ya fallasa sirrin da suke boyewa

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tun a watan Fabrairu ASUU ta shiga yajin aiki kan rashin cika alkawari da ke cikin yarjejeniya da ta yi da gwamnatin tarayya masu alaka da kudin inganta jami'o'i da allawus da albashi.

A hirar da aka yi da Osodeke a ranar Alhamis a Arise TV, ya ce jami'un da ke karkashin kungiyar suna yajin aiki har yanzu.

Kalamansa:

"Idan kana bada bayanai, ka duba asalin abin, Jami'ar Jihar Kwara ba mamba na ASUU bane, an dakatar da jami'ar Osun saboda rashin da'a, kana iya dubawa. LASU, da ka kira. Muna kotu da LASU saboda ta kori dukkan shugabannin mu shekaru biyar da suka wuce don haka ba su yajin aikin kuma gwamnatin Jami'ar Ekiti na da damar bude jami'ar kamar yadda ya faru a Jami'ar Jihar Gombe, Yobe da Jami'ar Jihar Kaduna.
"Don haka, kada ka bada misali da su, ba su da wani tasiri. Ka yi magana kan abin da ke da muhimmanci, Jami'ar Ibadan ya yajin aiki? Jami'ar Najeriya ta Nsukka (UNN) na yajin aiki? Jami'ar Ahmadu Bello (ABU) na yajin aiki? Jami'ar Bayero ta Kano na yakin aiki? Jami'ar Maiduguri da Jami'ar Legas na yajin aiki? Mu yi magana kan jami'o'i na gaskiya, ba wadannan na bogin ba."

Kara karanta wannan

Da duminsa: ASUU Reshen UNIZIK ta Ayyana Yajin-Aikin Sai Baba ta Gani

Martanin wasu jami'o'i

Mahukunta jami'ar Jihar Ekiti (EKSU) sun mayar da martani ga Mr Osodeke, inda suka yi tir da kiransu jami'ar bogi suka kuma nemi ya janye maganar ya basu hakuri.

shugaban sashin watsa labarai, Bode Olofinmuagun ya ce:

"Muna kira ga Farfesa Osodeke ya yi dattaku ya janye maganar da ya fada mara dadi ya bada hakuri ba tare da bata lokaci ba."

Sanarwar ta kara da cewa EKSU a yanzu ita ce jami'a ta 14 cikin jerin jami'o'i da ke kan gaba a Najeriya kuma ta biyu cikin jami'o'in jiha a cewar kididdigar Webometrin, Premium Times ta rahoto.

Ita ma jami'ar Jihar Kaduna ta yi tir da kalaman na Shugaban ASUU tana mai cewa abin kunya ne a ji irin wannan kalaman daga bakin shugaba kamansa.

Yajin Aikin ASUU: Ba Dole Ne Sai Kowa Ya Yi Digiri Ba, In Ji Gwamnan APC

Kara karanta wannan

Mun ki din: ASUU ta yi martani kan tayin iyayen dalibai na tara musu N10,000

A wani rahoton, gwamnan Jihar Ebonyi kuma shugaban kungiyar gwamnonin Kudu maso Gabas, David Umahi ya ce ilimin Jami'a fa ba na kowa da kowa bane, rahoton The Punch.

Umahi ya jadada cewa ba adalci bane a yi tsammanin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta ciyo bashin fiye da Naira tiriliyan 1 don biyan bukatun ASUU.

Asali: Legit.ng

Online view pixel