Labour Party: Muna Da Mambobi Miliyan 22, Ba A Soshiyal Midiya Kawai Aka San Mu Ba

Labour Party: Muna Da Mambobi Miliyan 22, Ba A Soshiyal Midiya Kawai Aka San Mu Ba

  • Jam'iyyar Labour Party, LP, ta ce ita ce za ta lashe kujeru a babban zaben shekarar 2023 mai zuwa
  • Arabambi Abayomi, sakataren jam'iyyar na kasa ya ce suna da magoya baya masu katin zabe har guda miliyan 22
  • Abayomi ya ce yan Najeriya sun gaji da jam'iyyar APC, sun kuma san Peter Obi da Labour Party ne za su kawo musu canjin da suke bukata

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Legas - Jam'iyyar Labour Party ta ce ita ba jam'iyya bace ta soshiyal midiya kawai, ta kuma sha alwashin ita za ta lashe zabukan 2023.

Sakataren jam'iyyar na kasa, Arabambi Abayomi, wanda ya bayyana hakan a Legas ya ce, suna da mambobi masu rajitsa fiye da miliyan 22, Daily Trust ta rahoto.

Peter Obi.
Labour Party: Muna Da Magoya Baya Miliyan 22, Ba A Soshiyal Midiya Kawai Muke Ba. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Ya ce yan Najeriya na neman canji saboda jam'iyyar All Progressives Congress, APC, mai mulki ta gaza cika alkawurran da ta yi wa mutane.

Kara karanta wannan

Magajin Buhari: Wani Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Ya Magantu Kan Yuwuwar Haɗa Kai Da Wata Jam'iyya a 2023

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kalamansa:

"Mu ba jam'iyyar soshiyal midiya bane. Mutanen da ke rally na jam'iyyar mu a jihohi yan adam ne. Muna sabon abin yayi, jam'iyyar da za ta canja Najeriya daga kasa mai siyo kayayaki zuwa kasa mai fitar da kaya zuwa kasashen waje.
"A yanzu da na ke maka magana, idan aka yi la'akari da kungiyoyin tallafi da suka yi wa mambobinsu rajista da jam'iyyar mu da katin zabensu da lambobin waya, muna da masu zabe guda miliyan 22."

Ya cigaba da cewa:

"Muna sa ran wasu za su shigo zuwa Disamba, yan Najeriya na son canji; sun sha wahala kuma sun san wanda suke son ya jagorance su. Kana iya gani a duk Najeriya, tafiyar na kara girma saboda Peter Obi ne dan takarar da yan Najeriya suka amince da shi. Yan Najeriya na neman canji mai kyau."

Asali: Legit.ng

Online view pixel