'Dan Takarar Shugaban Ƙasa Na SDP Ya Yi Magana Kan Hada Kai Da Wata Jam'iyya a 2023

'Dan Takarar Shugaban Ƙasa Na SDP Ya Yi Magana Kan Hada Kai Da Wata Jam'iyya a 2023

  • Ɗan takarar shugaban ƙasa karƙashin inuwar SDP ya ce jam'iyyarsa ba zata yi haɗin guiwa da kowace jam'iyya ba a zaɓen 2023
  • Prince Adewole Adebayo, da ke fatan ɗare wa kujerar Buhari a 2023 ya ce duk da ana gani ba su tabuka komai ba zasu shiga zaɓe
  • Ya kuma kara da cewa ko da babu wanda ya yi to zai bayyana wa Najeriya adadin dukiyar da ya mallaka

Abuja - Yayin da zaɓen 2023 ke tunkaro wa, Prince Adewole Adebayo, mai neman kujarar shugaban ƙasa a jam'iyyar SDP, ya ce jam'iyyarsa ba zata yi maja da wata jam'iyyar siyasa ba duk da ana kallon ba zata tabuka komai ba.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa, yayin da yake zanta wa da manema labarai, Adebayo, dake fatan gaje kujerar Buhari, ya ce duk rintsi zasu fafata a zaɓen 2023 domin suna da niyya mai kyau.

Kara karanta wannan

2023: Ƙungiyar Mayu Da Matsafa Ta Najeriya Ta Yi Magana Mai Ƙarfi Kan Tikitin Musulmi Da Musulmi Na APC

Prince Adewole Adebayo.
'Dan Takarar Shugaban Ƙasa Na SDP Ya Yi Magana Kan Hada Kai Da Wata Jam'iyya a 2023 Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

A kalamansa, ɗan takarar ya ce:

"Ba zamu kai labari ba amma ba zamu taɓa shiga tattaunawar haɗin guiwa ko yin maja tare da kowace jam'iyyar siyasa ba a halin da ake ciki yanzu."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce duba da lashe zaɓen shugaban ƙasa da ya gabata a 2023 wanda aka soke, jam'iyyar ta jima da kafuwa a tarihi kuma zata taimaka wajen tsamo Najeriya daga taɓarɓarewar tattalin arziki, siyasa da tsadar rayuwar da ake ciki.

Ɗan takarar kujera lamba ɗaya a Najeriya, wanda ya shirya fafatawa da manyan jam'iyyu, ya roki ƴan Najeriya da su mara wa jam'iyyar SDP baya a zaɓe mai zuwa.

Zan bayyana dukiyata a Oktoba - Adebayo

Mista Adebayo, ya ce zai bayyana wa ƴan Najeriya dukiyar da ya mallaka a Octoba ko da babu ɗan takarar shugaban ƙasan da zai yi haka.

Kara karanta wannan

Magajin Buhari: Sakamakon Zaɓen 2023 Zai Gigita 'Yan Najeriya, Tsohon Ɗan Majalisa

Ya ce ya nemi ƙungiyar da ke fafutukar kare hakkin mutane SERAP domin ta jawo hankalin sauran ƴan takarar kan lamarin, amma ba bu wanda ya ɗauki ƙalubalen.

A wani labarin kuma Ɗan Takarar Gwamna A PDP Ya Fice Daga Jam'iyyar, Ya Samu Tikitin Takara a 2023

Wani da ya nemi tikitin takarar gwamnan Ogun a inuwar PDP ya nuna fushinsa a fili, ya sauya sheƙa zuwa PRP.

Farfesa Olufemi Bamgbose, ya samu tikitin takarar gwamna a sabuwar jam'iyyarsa da zai ba shi damar shiga zaɓen 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel