2023: Bangaren Wike Ta Bada Sunan Wanda Ta Ke So A Nada Shugaban PDP Na Kasa

2023: Bangaren Wike Ta Bada Sunan Wanda Ta Ke So A Nada Shugaban PDP Na Kasa

  • Tawagar gwamnan Jihar Rivers Nyesom Wike ta mika sunan Taofeek Arapaja a matsayin wanda ta ke son a nada shugaban riko na PDP na kasa
  • Kungiyar ta ce cikin sharrudan da ta ke son a cika mata kafin ta goyi bayan dan takarar shugaban kasa Atiku Abubakar shine Iyorchia Ayu ya sauka daga shugabancin jam'iyyar
  • Gwamna Wike ya ragargaji tsohon gwamnan Jihar Jigawa Sule Lamido kan cewa da ya yi babu bukatar a bashi hakuri don ba a yi masa laifi ba

Bangaren gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike, a rikicin jam'iyyar PDP da ake yi suna bukaci a nada Taofeek Arapaja a matsayin shugaban jam'iyyar wucin gadi.

Premium Times ta rahoto cewa a ranar Juma'a a yayin taron da tawagar ta yi da dan takarar jam'iyyar Atiku Abubakar, ta bukaci murabus din shugaban jam'iyyar na kasa, Iyorchia Ayu, a matsayin sharadi na cigaba da tattaunawa da Atiku idan yana son goyon bayansu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Bayan Ganawa Da Atiku A Birtaniya, Wike, Ortom Da Ikpeazu Sun Dira A Port Harcourt

Arapaja da Atiku da Wike
2023: Bangaren Wike Ta Bada Sunan Wanda Ta Ke So A Nada Shugaban PDP Na Kasa. Hoto: @PremiumTimesNG.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mambobin kungiyar wadanda suka hallarci taron da aka yi a Landan sun hada da Gwamna Samuel Ortom na Benue, Seyi Makinde na Oyo, Okezie Ikpeazu na Abia da tsohon gwamnan Cross Rivers, Donald Duke, Segun Mimiko na Ondo da Ibrahim Dankwambo na Gombe.

Tawagar ta bada dalilai biyu na neman murabus din Ayu:

  • Na farko shine rashin daidaito a shugabancin jam'iyyar duba da cewa dan arewa ke da dan takarar shugaban kasa da kuma shugaban jam'iyya.
  • Na biyu kuma shine raba kan jam'iyya da Mista Ayu ke yi tun bayan zamansa shugaba suna mai cewa ba su gamsu da salon mulkinsa ba.

Tawagar ta Wike ta yi imanin Atiku zai iya lalaba Ayu ya yi murabus saboda abokai ne kuma shugaban jam'iyyar ya goyi bayan takararsa a zaben fidda gwani, Premium Times ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Ainihin Sababin Rikicin Wike Da Atiku, Jigon Jam'iyyar PDP Ya Yi Bayani

Wanene Arapaja?

Mista Arapaja tsohon mataimakin gwamna ne a jihar Oyo kuma mataimakin shugaban jam'iyyar na shiyyar kudu maso yamma.

Na hannun daman Gwamna Makinde ne, daya cikin gwamnonin da ke tawagar Wike.

Yankin Kudu maso Yamma bai taba fidda shugaban jam'iyya na kasa ba PDP.

Kungiyar ta bukaci Arapaja ya rike ofishin na wucin gadi har zuwa bayan babban zaben 2023 lokacin da jam'iyyar za ta iya zaben shugaba mai cikakken iko.

Wike: Sule Lamido Da Abokansa Ne Suka Kayar Da PDP A Zaben 2015

A wani rahoton, gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike ya yi shagube ga tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, yana mai cewa ba shi da wata tasiri a siyasar yanzu, The Punch ta rahoto.

Lamido yayin da ya ke magana a shirin Politics Today na Channels Television a daren ranar Talata ya ce babu bukatar yin sulhu tsakanin Wike da Atiku Abubakar domin babu wanda ya yi wa gwamnan na Rivers laifi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel