'Sako Daga Allah' Wani Babban Malami Ya Bayyana Sunan Wanda Zai Gaji Buhari a 2023

'Sako Daga Allah' Wani Babban Malami Ya Bayyana Sunan Wanda Zai Gaji Buhari a 2023

  • Wani Malami ya bayyana maganar Manzanci cewa ɗan takarar APC, Bola Tinubu, ne zai gaji shugaba Buhari a zaɓen 2023
  • A shekarar 2019, Malamin Cocin ya yi hasashen shugaba Buhari zai lashe zaɓe karo na biyu, haka Sanata Omo-Agege
  • Malaman Coci sun saba tsoma baki kan harkokin siyasa a Najeriya, inda wasu ke faɗin mutanen da zasu samu nasara

Delta - Wani babban Malamin addinin kirista da ake wa laƙabi da, "Prophet Coming of the Lord" wato manzanci daga Allah ya bayyana yadda zata kaya tsakanin yan takara a babban zaɓen 2023.

Vanguard ta tattaro cewa Malamin na Cocin 'the Lord of Paradise' ya ce ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, shi ne zai lashe zaɓen 2023 da ke tafe.

Kara karanta wannan

Jigon APC ya Jero Abubuwan da za su Hana Atiku Abubakar Samun Nasara a 2023

Bola Ahmed Tinubu.
'Sako Daga Allah' Wani Babban Malami Ya Bayyan Sunan Wanda Zai Gaji Buhari a 2023 Hoto: Asiwaju Bola Tinubu/facebook
Asali: Facebook

Malamin ya yi wannan furucin ne yayin da yake zantawa da manema labarai a gidansa a Otokutu, kusa da Warri, jihar Delta.

Ya ce yayin wata Ibadan da ya gudanar a baya- bayan nan, Allah ya faɗa masa abubuwa da dama da zasu faru game da zaɓen mai zuwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Babban Malamin, wanda a 2019, ya yi hasashen shugaba Buhari, zai lashe zaɓe, haka zalika mataimakin shugaban majalisar Dattawa, Sanata Omo Agege, ya ce Najeriya na da nagartattun mutane maza da mata da zasu iya shugabanci.

Babba Malamin mai dogon gemu ya ce:

"Zan faɗa muku abinda Allah ya gaya mun game da zaɓen 2023, kamar yadda na faɗi maganar Manzanci gabanin zaben fidda gwanin APC cewa mutumin da ake kira Jagaban ne zai yi nasara, Na tambayi Ubangiji waye Jagaban?"
"Meyasa Kake yawan magana kan Jagaban? Ubangiji ya gaya mun ba ya duba zahiri yana amfani da aiki ne a aikace, mutumin nan ya shugabanci Legas, ya maida jihar babban wuri."

Kara karanta wannan

'Yan Majalisu Biyu da Dubbannin Mambobin APC Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a Jihar Arewa

"Ya gayamun Alkairin da ya gani a APC, jam'iyyar ce zata lashe zaɓen shugaban Najeriya. Ba wannan kaɗai ba, mutumin (Tinubu) ya sha wahala wajen ɗaga mutane su zama shugabanni, Allah ya yi Alƙawarin ɗaga shi zuwa shugaban ƙasa."

Zamu ja hankalin yan Najeriya su zaɓi Tinubu - Adamu

A wani labarin kuma Shugaban APC ya ce a halin da ake ciki, Tinubu da Shettima ne zaɓin da ya dace da Najeriya a 2023

Shugaban jam'iyyar All Progressive Congress APC, Sanata Abdullahi Adamu, ya ce takarar mabiya addini ɗaya da jam'iyyarsa ta cike, shi ne abinda yan Najeriya ke bukata a halin da ake ciki.

Da yake hira da BBC Hausa , Adamu ya bayyana cewa takarar Musulmi da Musulmi, wata babbar dabara ce ta APC domin ta lashe zaɓen 2023 da ke tafe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel