2023: Musulmi da Musulmi Ne Ya Dace Da Najeriya a Yanzu, Adamu

2023: Musulmi da Musulmi Ne Ya Dace Da Najeriya a Yanzu, Adamu

  • Sanata Abdullahi Adamu, shugaban APC na ƙasa ya ce a halin da Najeriya ke ciki Tinubu da Shettima ne suka dace da ita
  • Tsohon gwamnan Nasarawa ya ce dabara ce ta sanya APC haɗa Musulmi da Musulmi, kuma zasu yi kokarin fahimtar da mutane
  • Bola Tinubu, ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar APC ya zaɓi Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Shugaban jam'iyyar All Progressive Congress APC, Sanata Abdullahi Adamu, ya ce takarar mabiya addini ɗaya da jam'iyyarsa ta cike, shi ne abinda yan Najeriya ke bukata a halin da ake ciki.

Da yake hira da BBC Hausa, Adamu ya bayyana cewa takarar Musulmi da Musulmi, wata babbar dabara ce ta APC domin ta lashe zaɓen 2023 ɗa ke tafe.

Sanata Abdullahi Adamu.
2023: Musulmi da Musulmi Ne Ya Dace Da Najeriya a Yanzu, Adamu Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Ɗan takarar shugaban ƙasa ƙarkashin inuwar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya zaɓi tsohon gwamnan Borno, Sanata Kashim Shettima, a matsayin abokin takararsa.

Kara karanta wannan

2023: Dalilin da Yasa NNPP Ba Zata Iya Cika Wa Shekarau Bukatarsa Ba, Kwankwaso

Daily Trust ta rahoto cewa wannan zaɓi ya ta da tarnaƙi a tsakanin wasu jiga-jigan jam'iyyar APC da wasu yan Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Adamu ya ce:

"Duba da yanayin da Najeriya ke ciki, ba zaka iya gamsar da kowa ba. Haka Demokaraɗiyya ta kunsa kowa na da yancinsa amma a wajen mu, musulmi da musulmi ne ya dace da Najeriya a yanzu."
"Amma ba zamu yi ƙasa a guiwa ba, zamu yi aiki tukuru don fahimtar da ƴan Najeriya su goyi bayan tikitin Tinubu da Shettima. Kowace jam'iyya na da dabarunta, mu kuma wannan ce dabarar da muke ganin zata ɓulle mana."

Matsalolin da ske ciki ba zasu dakatar da mu ba - Adamu

Adamu ya ƙara da cewa matsalar tsaro da taɓarɓarewar tattalin arzikin da Najeriya ke fama da su ba zasu hana jam'iyyar APC lashe zaɓe ba.

Kara karanta wannan

Luguden Wuta: Sojoji Sun Hallaka Ƙasurguman Yan Ta'adda da Yawa a Yankuna Uku Na Arewa

"Eh, akwai matsalar tsaro a ƙasa kuma kowace ƙasa na da nata kalar matsalar tsaron. kafafen watsa labarai ba su yaɗa kokarin gwamnati yadda ya kamata."

A wani labarin na daban kuma cikin ruwan sanyi yan Najeriya zasu dangwala wa APC ta lashe zaɓen 2023 a cewar gwamnan Katsina

Gwamnan Aminu Masari na jihar Katsina ya ce masu cewa APC ba zata kai labari ba a 2023 zasu sha kunya.

Gwamnan ya kaddamar da ɗakin kwanan ɗalibai da aka raɗa wa sunansa a jami'ar Al-Hikmah da ke jihar Kwara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel