Rayuwata Na Fuskantar Hadari Saboda Ina Ja da Gwamna – Mace Mai Takarar Sanata

Rayuwata Na Fuskantar Hadari Saboda Ina Ja da Gwamna – Mace Mai Takarar Sanata

  • Mrs Ann Agom-Eze ta bayyana halin da ta ke ciki tun da ta tsaya neman zama Sanata a Kudancin jihar Ebonyi a zaben 2023
  • Ann Agom-Eze ta shaidawa manema labarai cewa fito-na-fito da Gwamna David Umahi a APC ya jefa rayuwata a cikin hadari
  • ‘Yar siyasar ta nemi tuta ganin cewa da fako Gwamnan Ebonyi ya shiga zaben fitar da gwanin shugaban kasa a jam’iyyar APC

Ebonyi - A wata hira da aka yi da ita a jaridar Punch, Ann Agom-Eze ta bada labarin irin halin da ta shiga saboda ta na harin zama Sanata a jihar Ebonyi.

Ann Agom-Eze ta ce ta shiga takarar Majalisar Dattawa ne ganin Mai gidanta ya nemi kujerar Gwamna da ta Sanata a Ebonyi, amma bai kai labari ba.

Kara karanta wannan

Shiga siyasa: Matasa a Abuja sun kama wani Bishap, sun lakada masa dukan tsiya

A cewar ta, ta shiga siyasa ne bayan tayi ritaya a matsayin sakataren din-din-din a gwamnati. Sannan, tayi gado daga mahaifinta, wanda ya rike mukami.

Duba da wadannan abubuwa, Ann Agom-Eze ta tsaya takarar zama Sanata a karkashin jam’iyyar APC domin wakiltar mazabar Kudancin Ebonyi.

Manema labarai sun nemi jin yadda aka samu sabani tsakanin Agom-Eze da Mai girma David Umahi, domin an san irin alakar da ke tsakaninsu a baya.

Mai neman takarar Sanatar tace babu sa-in-sa tsakaninta da Gwamna, illa iyaka ta shiga takara a APC domin Gwamnan ya nemi tikitin shugaban kasa ne.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Princes
Princess Ann Agom-Eze Hoto: www.vanguardngr.com
Asali: UGC

A sabuwar dokar zabe kuwa, ba zai yiwu mutum daya ya shiga takara biyu a lokaci guda ba, don haka tsohuwar ma’akaciyar ta hari tikitin APC a zaben 2023.

Danuwar Gwamna ya janye takara

Kara karanta wannan

Sulhun Atiku da Wike: Bayan Zaman Sa'o'i 4 Ranar Juma'a, Har Yanzu An Gaza Cimma Matsaya

Kamar yadda Sun ta kawo labari, bayan zaben fitar da gwani sai ta ji ‘danuwan gwamnan wanda ya samu tikitin Sanata a APC, ya janye masa takararsa.

Nan take Agom-Eze ta kalubalanci matakin da jam’iyyar APC ta dauka, a dalilin haka INEC ba ta fito da sunan ‘dan takaransu na Sanatan Kudancin Ebonyi ba.

Daga baya an yi ta shari’a a kotu, har Alkalai suka bada umarni ga jam’iyya ta shirya sabon zaben fitar da gwanin Sanata na mazabar Kudancin jihar Ebonyi.

A zaben da aka sake ne aka yi waje da Agom-Eze, aka ayyana Umahi a matsayin ‘dan takara. An rahoto wannan Baiwar Allah tana cewa sam ba za ta yarda ba.

Ina ganin ta kai na - Agom-Eze

Har yau, ‘yar siyasar ba ta iya zuwa jihar Ebonyi ba saboda barazanar da manya suke yi mata, a cewarta ta kai ana zuwa kauyen Ebubeagu domin a cafke ta.

Kara karanta wannan

Shehu Sani: Yadda Gwamna El-Rufai Yake Taimakawa Wajen Jawo Matsalar Tsaro

Daga lokacin da ta fara neman takarar Sanata, Agom-Eze tace babu wulakancin da ba ta gani, abin ya kai an dakatar da fanshonta, ana tura mata ‘yan sanda.

Tinubu zai san makomarsa

An ji labarin Action Alliance ta dauki hayar Lauya, tayi karar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu mai neman zama Shugaban Najeriya a APC a zabe mai zuwa.

Action Alliance ta na so a hana Tinubu yin takara, kuma an sa ranar da za a yi shari'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel