Shugabar Matan PDP da Daruruwan Mambobi Sun Sauya Sheka Zuwa APC a Kebbi

Shugabar Matan PDP da Daruruwan Mambobi Sun Sauya Sheka Zuwa APC a Kebbi

  • Jam'iyyar APC a jihar Kebbi ta kara karfi tare da sauya sheƙar wasu ɗaruruwa mambobin PDP a shiyyar Kebbi ta tsakiya
  • Shugabar Matan PDP ta shiyyar, Yar Sakkwato Jega, tare da wasu ɗaruruwan masoyanta sun rungumi tsintsiya
  • Manyan jiga-jigan jam'iyyar APC mai mulkin jihar sun halarci taron bikin sauya shekar wanda aka gudanar ranar Laraba a Birnin Kebbi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kebbi - Shugabar matan jam'iyyar PDP reshen shiyyar jihar Kebbi ta tsakiya, Yar Sakkwato Jega, ta sauya sheƙa zuwa jam'iyyar All Progressive Congress, APC.

Jaridar Daily Nigerian ta rahoto Misis Jega na bayyana haka a wurin wani taro da aka shirya dominta ranar Laraba a Birnin Kebbi, babban birnin jihar.

Shugabar matan PDP.
Shugabar Matan PDP da Daruruwan Mambobi Sun Sauya Sheka Zuws APC a Kebbi Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Ta ƙara da cewa ta yanke shawarin tattara kayanta ta bar jam'iyyar ne saboda rashin adalci da kuma gurɓataccen shugabanci.

Kara karanta wannan

Kungiyar 'yan Arewa: Kamata ya yi Shettima ya hakura da takara da Tinubu saboda dalilai

A jawabinta, ta ce ta zaɓi rungumar tsintsiya a APC ne saboda ɗumbin nasarorin da gwamna Atiku Bagudu ya samu a mulkinsa, inda tace ta shiga jam'iyyar tare da magoya bayan sama da 800.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Na shafe tsawon shekaru a PDP, ba su da wani abu da zasu nuna wa al'umma kuma an maida mu ba a bakin komai ba."
"Na sha amfani da kuɗaɗe na don ɗaga jam'iyya, amma banga wani canji tattare da mutane na ba, musamman mata yan uwana da nake wakilta."
"Gabanin sauya sheƙa ta, kananan hukumomi Takwas ne a ƙarƙashina a jam'iyyar PDP, na tattara mafiya yawa masoya na mun bar jam'iyyar tare."

- Yar Sakkwato Jega.

Legit.ng Hausa ta gano cewa wasu daga cikin jiga-jigan da suka halarci taron sun haɗa da shugaban APC na jiha, Abubakar Kana-Zuru, shugaban ƙungiyar dattawan APC, Sani Zauro, da mai taimaka wa gwamna (PA), Faruk Musa Yaro.

Kara karanta wannan

Rashin Tsaro: Yan Majalisar Dokokin Jihar Katsina Zasu Sa Labule da Gwamna da Shugaba Buhari

A wani labarin kuma Daga Karshe, Shugaban APC Na Kasa Ya Yi Magana Kan Shirin Tsige Shugaba Buhari

Shugaban APC, Abdullahi Adamu, ya ce yunkurin yan majalisar tarayya na tsige Buhari wani cigaba ne abun takaici da nadama.

Tsohon gwamnan jihar Nsarawan ya ce haka na faruwa a kowace kasa amma har waɗan da suka kirkiri lamarin sun gudu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel