APC Za Ta Fara Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa a Ranar 28 Ga Satumba

APC Za Ta Fara Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa a Ranar 28 Ga Satumba

  • Majiyoyi daga jam'iyyar APC sun bayyana cewa, za a fara gangamin yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar nan kusa
  • Jam'iyyar APC a watan Afrilu ta saryar da ikon kwamitin na NEC ga kwamitin NWC domin dinke wasu abubuwa a jam'iyyar
  • Jam'iyyun siyasar Najeriya na gi gaba da shirye-shirye domin tunkarar zaben 2023 mai zuwa nan da watanni bakwai

FCT, Abuja - Bayan wasu sauye sauyen tsare-tsare, jam’iyyar APC ta bayyana shirin fara gangamin yakin neman zaben shugaban kasa a ranar 28 ga watan Satumba.

A yau ne aka shirya gudanar da taron kwamitin ayyuka na kasa (NWC) na APC karkashin jagorancin Sanata Abdullahi Adamu, domin yanke shawara kan ranar da kuma shirya taron kwamitin zartarwa (NEC) na jam’iyyar APC na kasa.

Bayan saute, APC za ta fara gangamin zaben 2023
APC Za Ta Fara Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa a Ranar 28 Ga Satumba | Hoto: thisdaylive.com
Asali: UGC

Bincike ya nuna cewa a taron karshe da NEC ta APC ta gudanar a watan Afrilu, ta mika ragamar mulki ga kwamitin ta na NWC na tsawon kwanaki 90, Tribune Online ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tinubu na kawai karfe 4 na dare bai yi barci ba yana aiki saboda tsananin kwazonsa , Shugaban matasan APC Dayo Isarel

Wata majiyar jam’iyyar ta bayyana cewa taron na gaggawa da NEC za ta yi ya zama dole ne domin wancan kwamitin ya sabunta ikonsa da aka mika wa NWC karkashin jagorancin Sanata Adamu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bayan cikar kwanaki 90 din, wata majiya mai karfi ta shaida wa jaridar This day cewa, NWC ba za ta iya daukar muhimman shawarwari a madadin jam’iyyar ba ba tare da amincewar kwamitn na NEC ba.

Majiyar ta ce:

“Yayin da wa’adin watanni uku ya kare tun daga ranar 22 ga watan Yuli, NWC ba za ta iya daukar muhimman shawarwari a madadin jam’iyyar ba ba tare da amincewar NEC na, kuma bisa la’akari da yadda tsarin mulki ya tanada, wasu mambobin NWC na kokarin ganin an yi taron gaggawa na NEC."

Kamar yadda kudurorin taron NEC na watan Afrilu ya tanada kuma sakataren yada labaran jam’iyyar APC na kasa, Felix Morka, ya karanta wa manema labarai, ya bayyana cewa, an mika ikon NEC mai lamba 13(3)(ii)(iii) (iv)(v) da (vi) ga NWC na tsawon kwanaki 90.

Kara karanta wannan

APC Ta Faɗi Sunan Wani Gwamnan PDP Dake da Hannu a Matsalar Tsaron Jiharsa, Ta Nemi a Kayar da Shi a 2023

Don haka ne aka bai NEC ikon sauke ayyukan hukumar kamar yadda yake a shafi na 13.3 (ii) na kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC.

Gwamna Wike na Ribas: Ko da Kun Cire Ni a PDP Zan Tsinana Abin Alheri Ga Jama’a

A wani labarin, gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya ce ingantaccen shugabanci nagari bai da alaka kuma bai shafi jam’iyyun siyasa ba, Daily Trust ta ruwaito.

Wike ya bayyana haka ne a wajen bikin kaddamar da titin Ogbunuabali-Eastern Bypass wadda wani jigon jam’iyyar APC Sanata Aliyu Wamakko ya halarta a jiharsa a ranar Talata.

Gwamnan ya ce ba daidai ba ne mutane su yi tunanin cewa shugabanci aiki ne na jam’iyyun siyasa, yana mai cewa aiki ya shafi tunani ne na mutum.

Asali: Legit.ng

Online view pixel