Ministan Buhari Ya Yi Wa Dino Melaye Alkawarin Wata Babban Alfarma Idan Ya Kammala Wa'adinsa A 2023
- Ministan Buhari Ya Yi Wa Dino Melaye Alkawarin Wata Alfarma Da Zarar Ya Sauka Daga Mukaminsa A 2023
- Festus Keyamo, karamin ministan kwadago da ayyukan yi, ya yi wa Dino Melaye alkawarin da zai cika a shekarar 2023
- Ministan ya ce zai yi wa tsohon dan majalisar rajista a makarantar koyon waka don ya goge kamar sauran mawakan kasar
Keyamo da Melaye sun fara musayar maganganu tun bayan nada su a matsayin kakakin yakin neman zaben Bola Tinubu da Atiku Abubakar
Ba a fara kamfen din zaben shugaban kasa na shekarar 2023 ba a hukumance amma ana ta musayar maganganu tsakanin Sanata Dino Melaye da Minista Festus Keyamo.
A wani hira da aka yi da shi a Arise TV a ranar Litinin 8 ga watan Agusta, Keyamo ya yi ikirarin cewa yana kewan kotu kuma zai koma can da zarar wa'adinsa a matsayin karamin ministan kwadago da samar da ayyuka ya kare a 2023.
Ministan ya yi ikirarin cewa idan hakan ta faru, zai tabbatar ya yi wa Melaye rajista a makarantar waka, ya kara da cewa kakakin kamfen din na Atiku Abubakar yana bukatar malami sosai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Keyamo ya cigaba da cewa da tunda farko Melaye ya taho wurinsa, da yanzu ya yi nasara sosai a wakokinsa da barkwanci.
Ya yi alkawarin zai raini tsohon dan majalisar kamar yadda ya raini wasu mawaka da a yanzu suna moriyar sana'ar.
Kalamansa:
"Zan koma aikin lauya na bayan wa'adi na ta minista ta kare kuma zan tabbatar na yi wa Dino Melaye rajista a makarantar waka, yana bukatar hakan sosai."
A Aljanna Ne Kawai Ba Za A Samu Matsalar Tsaro Ba, Yanzu Kuma Duniya Muke, Ministan Buhari, Keyamo
A wani rahoton, Festus Keyamo, karamin ministan kwadago da samar da ayyuka, ya ce ba za a iya amfani da 'hare-haren' da aka kaiwa wasu sassan kasar ba a matsayin 'mizani' na cewa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta gaza.
Keyamo ya yi wannan jawabin ne a hirar da aka yi da shi a Channels Television a ranar Juma'a, The Cable ta rahoto.
A cikin yan makonnin baya-bayan nan, munanan hare-hare sun karu a sassan kasar har da babban birnin tarayya, Abuja.
Asali: Legit.ng