Yanzu-Yanzu: Masu zanga-zanga sun mamaye sakateriyar PDP, suna kira a tsige shugaban jam'iyya

Yanzu-Yanzu: Masu zanga-zanga sun mamaye sakateriyar PDP, suna kira a tsige shugaban jam'iyya

  • Wasu matasa na jam'iyyar PDP sun mamaye sakateriyar jam'iyyar a yau Laraba suna kira a tsige shugaban jam'iyya
  • Kotun ta ba da umarnin mayarwa wani dan takarar gwamna matsyain takarar gwamnan jihar Delta a wani zama
  • PDP ta gaza bin umarnin kotu, wannan yasa matasa suka fito domin nuna kin amincewarsu da shugabancin Ayu

A yau Laraba ne sakateriyar PDP ta cika makil da jama'a yayin da rikici ya barke a PDP kan tikitin takarar gwamna a jihar Delta a 2023.

Matasan PDP ne suka mamaye sakatariyar jam'iyyar ta kasa suna neman shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Iyorchia Ayu ya yi murabus nan take.

Rahoton Vanguard ya ce, an ga magoya bayan jam’iyyar a karkashin kungiyar Concerned Deltans for Good Governance a dandalin Wadata Plaza, domin nuna rashin jin dadinsu.

Kara karanta wannan

Elrufai Ya Ce APC ta Riga Ta Nada Darakata Janar Na Kamfen Din Takarar Tinubu Da Shettima

Wata sabuwa: An nemi a tsige shugaban PDP nan take
Yanzu-Yanzu: Sakateriyar PDP ta dagule, 'yan zanga-zanga na kira a tsige shugaban jam'iyya | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Sun nuna damuwa kan abin da suka bayyana a matsayin kin bin umarnin babbar kotun tarayya ta korar Rt. Hon. Sheriff Oborevwori a matsayin dan takarar jam'iyyar PDP a zaben gwamna na shekara mai zuwa a Delta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Idan baku manta ba, umarnin kotu wanda mai shari’a Taiwo Taiwo ya bayar ya bayyana Olorogun David Edevbie a matsayin wanda aka zaba bisa doka kuma dan takarar jam’iyyar a zaben gwamna mai zuwa, inji TheCable.

Haka kuma ta umurci jam’iyyar PDP da ta mika sunan Edevbie zuwa ga hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), hakazalika INEC ta ba shi cikakken hakki da ya kamace shi a matsayin dan takarar jam’iyyar.

Akasarin masu zanga-zangar da suka yi dandazo domin neman jam'iyyar ta bi hukuncin mai shari'a Taiwo na dauke da kwalaye da rubuce-rubuce, kamar su:

Kara karanta wannan

Tsintsiya ta tsinke a Borno: Dan a mutun Tinubu ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP

"Ayu ba shi da kimar da zai sa PDP ta kai ga nasara", "Ku yi biyayya ga hukuncin kotun Abuja ta FHC", da dai sauran kalamai na nuna rashin jin dadi.

Da yake yiwa manema labarai jawabi yayin zanga-zangar, shugaban kungiyar, Chris Anthony, ya yi zargi cewa, Ayu zai jagoranci jam’iyyar zuwa ga halaka.

Sauya sheka: Ta karewa APC a Borno yayin da Dan a Mutun Tinubu ya koma PDP

A wani labarin, an kuma, mai yiwuwa dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC mai mulki, Bola Ahmed Tinubu ya sake fuskantar koma baya a jirgin yakin neman zabensa biyo bayan ficewar daya daga cikin abokan tafiyarsa.

Hon. Abdu Musa Msheliza, tsohon dan majalisar wakilai kuma mamba a kungiyar goyon bayan Tinubu a jihar Borno ya sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

A cewar rahoton, Msheliza ya bayyana cewa, ficewar sa daga APC ya samo asali ne daga yana son a samar da yanayi da za kawo yi adalci, daidaito da kuma shawarwarin a tafiya da harkokin siyasa.

Kara karanta wannan

Daliban Najeriya sun shiga tasku: ASUU ta tsawaita yajin aikinta zuwa karin wasu makwanni masu yawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel