Jigon Jam'iyyar APC a Kano, Injiniya Bashir, Ya Fita Daga Jam'iyyar

Jigon Jam'iyyar APC a Kano, Injiniya Bashir, Ya Fita Daga Jam'iyyar

  • Injiniya Bashir I. Bashir, jigo a jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a Jihar Kano ya yi murabus daga jam'iyyar
  • Bashir, tsohon abokin siyasa na tsohon gwamnan Kano Ibrahim Shekarau ya sanar da ficewarsa ne cikin wasikar da ya aika wa ciyaman na APC a gundumar Alawa
  • Tsohon dan takarar gwamnan na jam'iyyar Peoples Democratic Movement, PDM, ya shaidawa manema labarai cewa nan da kwana kadan zai sanar da matakin siyasa na gaba da zai dauka

Jihar Kano - Tsohon mai neman takarar gwamnan kuma jigo a jam'iyyar APC, Bashir I. Bashir ya fice daga jam'iyyar mai mulki, rahoton Daily Nigerian.

Bashir I. Bashir.
Jigon Jam'iyyar APC a Kano, Injiniya Bashir, Ya Fita Daga Jam'iyyar. Hoto: @daily_nigerian.
Asali: Twitter

A cikin wasika da ya aike wa shugaban jam'iyyar na APC a gundumar Alawa, karamar hukumar Gaya a Jihar Kano, Mr Bashir ya gode wa shugaban jam'iyyar bisa goyon baya da hadin kai da ya bashi.

Kara karanta wannan

2023: Awanni Bayan Kaddamar Da Abokin Takarar Kwankwaso, Wasu Jami'an NNPP Sun Riga Mu Gidan Gaskiya

Nan da yan kwanaki zan bayyana jam'iyyar da zan koma, Bashir

Ya shaidawa yan jarida cewa nan da kwanaki kadan sai sanar da jam'iyyar da zai koma.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mr Bashir, wanda injiniya ne ya yi takarar gwamna a karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Movement, PDM.

A baya, tsohon na hannun daman tsohon gwamnan Jihar Kano, Ibrahim Shekarau ne a siyasance.

Zaben 2023: Jerin Sanatocin APC da Suka Sauya Sheka Zuwa PDP da Wasu Jam'iyyu

A wani rahoto, yayin da ake jiran zuwan ranar zaben shekarar 2023, wasu sanatotin jam'iyya mai mulki ta APC sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP da sauran jam'iyyun adawa.

Yawancin idan ba duka wadanda suka sha kaye a zaben fidda gwanin jam'iyyar APC sun sauya sheka bayan gaza samun tikitin tsayawa takara domin cigaba da tabbata a madafun iko ko tsayawa takarar gwamna a zaben shekarar 2023.

Kara karanta wannan

Hotunan fitattun 'yan siyasar Najeriya da hamshakan da suka halarci auren diyar Kashim Shettima

A kalla sanatoci bakwai na jam'iyya mai mulki ta APC sun sauya sheka zuwa ko dai PDP ko kuma wata jam'iyyar adawa kafin zabe mai karatowa na shekarar 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel