2023: Sabon sabani ya kunno kai a APC kan wanda Tinubu ya zaba mataimaki, Gwamna El-Rufa'i ya fusata

2023: Sabon sabani ya kunno kai a APC kan wanda Tinubu ya zaba mataimaki, Gwamna El-Rufa'i ya fusata

  • Sabon rikici ya kunno kai a jam’iyyar APC mai mulki kan zabar Kashim Shettima da Tinubu ya yi a matsayin abokin takara
  • Rahoto ya nuna cewa gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai bai ji dadin zabar Shettima da aka yi a kansa ba
  • Tun farko dai majiyoyi sun ce sunan El-Rufai da Shettima aka gabatarwa Tinubu don ya zabi daya amma sai ya yi biris da gwamnan na Kaduna

Rahotanni sun kawo cewa Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna bai ji dadin hukuncin da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Tinubu, ya yanke ba na zabar tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, a matsayin abokin takararsa.

Jaridar Daily Independent ta rahoto daga wasu majiyoyi cewa shugabancin APC na kokarin ganin ta sasanta lamarin a cikin gida ta yadda ba zai fita waje kamar na jam’iyyar PDP da gwamnan jijar Ribas, Nyesom Wike ba.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Dan Abacha ya rasa damar takarar gwamna, an zabi wani a madadinsa

Kamar yadda yake a yanzu, alaka ta yi tsami tsakanin Wike da dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar wanda ya sanar da Ifeanyi Okowa na jihar Delta a matsayin abokin takararsa.

Tinubu da El-Rufai
2023: Sabon sabani ya kunno kai a APC kan wanda Tinubu ya zaba mataimaki, Gwamna El-Rufa'i ya fusata Hoto: Nasir El-Rufai
Asali: Facebook

Majiyoyin sun ce an takaita jerin sunayen abokan takarar Tinubu tsakanin El-Rufai daga arewa maso yamma da Shettima daga arewa maso gabas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da mutane da dama suka fi raja’a kan cewa Tinubu zai zabi El-Rufai, kawai sai tsohon gwamnan na jihar Lagas ya sanar da Shettima a matsayin abokin takararsa.

Rahoton ya kuma kawo cewa an rubuta sunan Gwamna Simon Lalong na jihar Plateau cikin jerin sunayen koda Tinubu zai yanke shawarar yin tikitin Musulmi da Kirista.

Amma da ya tabbatar lallai Musulmi dan uwansa yake son zaba a matsayin abokin takara sai aka gabatar da sunan El-Rufai da Shettima amma sai Tinubu ya zabi tsohon gwamnan na Borno wanda ya kasance daya daga cikin masu yi masa biyayya ba tare da tuntubar gwamnonin ba.

Kara karanta wannan

Sha'awar cancanta ne Yasa muke Goyon bayan Tinubu maimakon Peter Obi - Matasan Ibo

Duk da wannan ci gaban, gwamnonin sun kawar da fushinsu daga idon duniya sannan suka halarci gangamin kamfen din dan takarar gwamnan jam’iyyar a zaben Osun. Kuma sai PDP ta yi nasara a zaben.

Majiyoyin sun ce:

“Irin halin da PDP ke ciki shine ke dawainiya da APC a yanzu. Gwamna El-Rufai bai ji dadi ba game da hukuncin da Asiwaju Bola Tinubu ya dauka. An aika masa da jakadu amma ya kore su."

Duk da haka, ya halarci gangamin kamfen din gwamnan Osun a makon jiya saboda bai da matsala da takwaransa, Oyetola.

Majiyoyin sun kuma ce:

“Amma ko shakka babu, ya yi fushi da Tinubu. Hakazalika wasu gwamnonin APC musamman na arewa sun tausayawa El-Rufai domin sun nanata cewa tunda sun mara ma Tinubu baya a zaben fidda gwani, toh lallai dole ya zabi daya daga cikinsu a matsayin abokin takara.
“Gwamnonin APC wadanda sune manyan masu ruwa da tsaki a jam’iyyar na ganin Tinubu ya ci zarafinsu ta hanyar sanar da Shettima, tsohon gwamna a matsayin zabinsa ba tare da tuntube su ba.”

Kara karanta wannan

Atiku Ya Bayyana Dalilin Da Ya Hana Shi Daukar Wike a Matsayin Mataimakin Sa

Sharhi kan kalubalen da ke gaban Tinubu daga Marubuci mai zaman kansa

Legit Hausa ta nemi jin ta bakin wani marubuci mai zaman kansa, Mallam Muhammad Auwal kan kalubalen da ke gaban Tinubu inda ya yi sharhi kamar haka:

“Masu iya magana sun ce "Ba anan take ba, wai an danne bodari ta kai" bayan lashe zaɓen fidda gwani da tsohon gwamnan jihar Legas, Sanata Ahmad Bola Tinubu yayi a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar APC, wani babban ƙalubale dake gabansa shi ne tabbatar da haɗin kan ƴaƴan jam'iyyar, musamman jiga jigan ƴaƴanta, masu a ji.
“Wannan mataki kuwa na da matuƙar muhimmanci duba da matakin da Tinubun ya ɗauka na zaɓo tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa, inda hakan ya harzuƙa wasu ƴaƴan jam'iyyar, musamman jiga jigan ƴaƴanta kiristoci ƴan Arewa sakamakon kallon da suke ma takarar Tinubu a matsayin takarace ta Musulmi da Musulmi.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Hotuna sun bayyana, Tinubu ya kaddamar da Shettima a Abuja

“A yanzu dai ana ta cecekuce da kuma ƴan gutsuri tsoma a cikin jam'iyya mai mulki, yayin da wasu tuni suka fara yin sallama da jam'iyyar domin nuna rashin amincewarsu da matakin.
“Baya ga manyan kiristocin jam'iyyar APC ƴan Arewa, wasu masu ruwa da tsaki a jam'iyyar da Tinubu zai sha fama dasu su ne mutanen da aka miƙa masa sunayensu domin ya zaɓo mataimakinsa daga cikinsu, wanda daga ciki akwai gwamnonin jam'iyyar, Sanatoci, tsofaffin gwamnoni da ministoci, inda daga cikinsu ya zaɓo Kashim.
“Akwai raɗe raɗin dake nuna yiwuwar wasu daga cikin waɗanda Tinubun ya tsallake zasu iya masa bore, ta hanyar ƙin goyon takarar tasa domin nuna ɓacin ransu da tsallakesu da yayi.
“Koda yake ɗan takaran na APC na da goyon bayan mafi yawan shuwagabannin jam'iyyar, amma abu ne mai kyau ya zauna da duk masu ƙorafe ƙorafe domin jin ta bakinsu tare da share musu kukansu ta yadda zasu tabbatar masa da goyon bayansu yayin da ake tunkarar zaɓen 2023 domin a gudu tare a tsira tare.

Kara karanta wannan

2023: Ba don ra'ayin kaina na zabi Shettima ba, Tinubu ya fadi dalilin zabo mataimakinsa

“Ba giringirin ba dai, ta yi mai!”

2023: Ba don ra'ayin kaina na zabi Shettima ba, Tinubu ya fadi dalilin zabo mataimakinsa

A gefe guda, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yi bayanin cewa ya zabi abokin takara daga cikin yan arewa marasa rinjaye ne saboda ci gaban kasar gabaki daya.

Tinubu ya bayyana hakan ne gabannin bayyana Alhaji Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa a hukumance a ranar Laraba a Abuja, jaridar Independent ta rahoto.

Tsohon gwamnan na jihar Lagas ya ce da ace yana tunanin samun tarin kuri’u ta hanyar amfani da kabilanci ne toh zai zabi mataimaki daga yankin arewa maso yamma ne domin a cewarsa ita ce ta fi yawan masu rijistan zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel