2023: Sowore Ya Bayyana Tsaffin Shugabanin Najeriya 3 Da Jigon Arewa Da Ke Goyon Bayan Peter Obi

2023: Sowore Ya Bayyana Tsaffin Shugabanin Najeriya 3 Da Jigon Arewa Da Ke Goyon Bayan Peter Obi

  • Peter Obi na cigaba da fuskantar zarge-zarge daga wasu yan siyasa gabanin babban zaben shekarar 2023
  • Daga cikin yan siyasan shine Omoyele Sowore, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar African Action Congress
  • Sowore, a wani rubutu da ya wallafa a shafin dandalin sada zumunta ya ce janar din soji masu murabus uku na goyon bayan Obi ciki har da tsohon shugaban kasa na mulkin soja

Twitter - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar African Action Congress kuma mawallafin Sahara Reporters, Omoyele Sowore, ya yi ikirarin cewa wasu manyan yan arewa da tsaffin shugaban kasa suna goyon bayan takarar Peter Obi.

Dan takarar na AAC ya lissafa tsaffin shugaban kasa uku na mulkin soja - Olusegun Obasanjo, Ibrahim Babangida da Abdulsalam Abubakar a matsayin 'iyayen gidan' Obi.

Kara karanta wannan

Musulmi da Musulmi: Kada ku yarda wani fasto ko limami ya fada maku wanda za ku zaba, Keyamo ga yan Najeriya

Peter Obi da IBB
2023: Sowore Ya Bayyana Tsaffin Shugabanin Najeriya 3 Da Jigon Arewa Da Ke Goyon Bayan Peter Obi. Hoto: @OfficialPOSG.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma ambaci tsohon mai bawa shugaban kasa shawara kan tsaro, Aliyu Gusau da shugaban kungiyar dattawan arewa na yanzu, Ango Abdullahi.

Wallafar ta ce:

"Olusegun Obasanjo, Ibrahim Babangida da Abdulsalam Abubakar da Ango Abdullahi ne 'iyayen gidan' Peter Obi, mutanen da suka lalata Najeriya suna ke tsaya masa. Kada Allah ya sa mu yi aiki da wadannan bata garin!."

Yan Najeriya sunyi martani kan zargin Sowore

Wallafar da dan takarar shugaban kasar na AAC ya yi ta janyo hankulan yan Najeriya a Twitter da Facebook.

A Facebook, Samuel Sokolayem ya rubuta:

"Allah ya baka iko da karfin mayar da hankali kan takararka. Ka kyalle batun wasu mutanen."

Solomon Ebenezer Nnadi ya rubuta:

"Idan wannan hanyar ce za su bi don shafe kurakurensu. An yafe musu muggan ayyukan da suka yi."

Kara karanta wannan

Tikitin Musulmi Da Musulmi Kaddara Ce Daga Allah, Shugaban APC, Adamu

Muhammadu Shamsudeen Abdullahi ya rubuta:

"Janar Babangida mutum ne da ba za ka iya yi wa wargi ba. Ka gode wa Allah ba shi da lokacin ka."

Sai Iyke Uwarfule ya rubuta:

"Suna goyon bayansa don sun san lokacinsu ya kure. Suna son daidaita tsakaninsu da Allah, don haka, hanya guda kawai shine su bamu Peter Obi a matsayin wanda zai wanke musu zunubansu don su samu rahama idan lokacinsu ya zo."

Asali: Legit.ng

Online view pixel