Shettima: Tsohon ‘Dan takarar Gwamna ya bar APC, yana neman kawo cikas

Shettima: Tsohon ‘Dan takarar Gwamna ya bar APC, yana neman kawo cikas

  • Tonye Princewill ya raba jiha da APC ganin Kashim Shettima ne ‘dan takaran mataimakin shugaban kasa
  • A yau Tonye Princewill ya rubuta takardar barin jam’iyya, ya ce ba zai iya kare Bola Tinubu da jam'iyyar ba
  • ‘Dan siyasar ya nuna wasu da-dama za su fice daga APC a reshen jihar Ribas a kan hana Kiristoci tikiti a 2023

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Rivers - Tsohon ‘dan takarar Gwamna a Ribas, Tonye Princewill ya tabbatar da ficewarsa daga jam’iyya mai mulki a sanadiyyar takarar shugaban kasa.

Jaridar Punch ta ce dalilin Tonye Princewill na barin jam’iyyar APC kamar yadda ya bayyana, shi ne tsaida Musulmi da Musulmi a zaben da za ayi a 2023.

‘Dan siyasar ya sanar da manyan jam’iyya murabus din na sa ne a wata wasika da ya aikawa shugaban PAC na mazabarsa da ke Buguma a garin Asar Toru.

Kara karanta wannan

Tikitin Tinubu/Shettima: Adamu Garba ya sake komawa jam’iyyar APC

Da yake bayani a wasikar da ya fitar a ranar Talata, 12 ga watan Yuli 2022, Princewill ya ce sam ba zai iya wanke jam’iyyarsa daga matakin da ta dauka ba.

A ra’ayin tsohon ‘dan takarar, ba ayi la’akari da sauran jama’a da aka hana kirista tikiti ba, a na shi hangen, ba za a ce babu Kiristan Arewa da ya dace ba.

Ya kamata Amaechi ya bar APC

The Nation ta ce Princewill ya godewa jagoransa watau Rotimi Amaechi na kokarin da ya yi masa a siyasa, ya ce an zo gabar da dolensa ya hakura da APC.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

'Yan Jam'iyyar APC
APC ta na kamfe a Ribas Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Baya ga haka, tsohon mai neman gwamnan ya ba Amaechi shawarar ya yi koyi da shi, ya na mai cewa bai dace Tinubu ya ki daukar Kirista daga Arewa ba.

Kara karanta wannan

Kwankwaso: Idan na rasa kujerar Buhari, kowa ma ya rasa, amma Tinubu ya samu

A halin da ake ciki a yau, jigon na APC yana ganin ko da APC ta yi nasarar lashe zabe da tikitin Musulmi da Musulmi, ba za ta ji dadin jagorantar al’umma ba.

APC ta sake yin rashi a Ribas

‘Ya ‘yan APC a Ribas sun san abin da ya dace, Princewill a takardar, ya ce bai ji dadin barin APC ba, amma hakan ya zama dole a irin yanayin da ya samu kan shi.

Mista Princewill wanda Attajirin ‘dan siyasa ne, kuma jigo a jam’iyyar APC, yana cikin na kusa da tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi a tafiyar siyasa.

A zaben 2015, Princewill ya nemi takarar gwamnan jihar Ribas a karkashin Labour Party, bayan nan ya koma APC, amma sai aka hana jam’iyyar takara a 2019.

Festus Keyamo a kan Musulmi da Musulmi

An ji cewa Asiwaju Bola Tinubu ya zabi Kashim Shettima ne ya zama abokin takararsa, wannan bai yi wa wasu dadi ba, musamman kiristocin jam’iyyar.

Amma sai ga rahoto cewa duk da Ministan kwadago Kirista ne, ya kare Bola Tinubu a kan dauko Sanata Kashim Shettima da ya yi, ya ce Sanatan ya cancanta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel