2023: Ɗan takarar shugaban ƙasa ya nesanta kansa da wani Hoto da aka nuna shi kan Sallaya

2023: Ɗan takarar shugaban ƙasa ya nesanta kansa da wani Hoto da aka nuna shi kan Sallaya

  • Tsohon gwamnan jihar Anambra kuma ɗan takarar shugaban kasa a 2023 ya nesanta kansa da Hoto da aka hangesa kan dardumar Sallah
  • Peter Obi ya ce Hotonsa da wasu suka ɗora kan sallayar Sallah ba dai-dai bane ko da kuwa sun yi da kyakkyawar niyya
  • Ana gani Obi ya zarce sauran yan takarar shugaban ƙasa yawan magoya baya a dukkan shafukan sada zumunta

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, ya nesanta kansa da wani hoton daddumar Sallah da aka ɗora Hotonsa, wanda ya fara jan hankali a kafafen sada zumunta ranar Jumu'a.

Vanguard ta ruwaito cewa duk da har yanzun ana kan gudanar da binciken asalin Hoton abun Sallan, Mista Obi, yayin martani kan lamarin ya nesanta kansa da tawagar yaƙin neman zaɓensa daga Hoton.

Kara karanta wannan

Peter Obi bashi da tsaurin ra'ayin addini kuma baya kyamar mutanen Arewa

Dan takarar shugaban kasa na LP, Peter Obi.
2023: Ɗan takarar shugaban ƙasa ya nesanta kansa da wani Hoto da aka nuna shi kan Sallaya Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Ya kuma bayyana cewa har cikin zuciyarsa yana girmama Addinin Musulunci da Musulmai kamar yadda ya ke girmana kowane Addini kuma a ko wane hali ba zai ci mutuncin kowane Addini ba.

Peter Obi ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Sanya Hoto na kan daddumar Sallah ba dai-dai bane ko da kuwa an yi da kyakkyawar niyya. Ba shi da alaƙa da tawagar yaƙin neman zaɓe na, ina matuƙar girmama Addinin Musulunci da sauran Addinai."

An matsa wa Fasto lamba kan Peter Obi

A wani cigaban kuma, babban Faston cocin Covenant Christian Nation, Poju Oyemade, ya sha matsin lamba bisa tilas ya goge rubutun da ya yi wanda ya caccaki matasan Najeriya da ke goyon bayan Peter Obi.

Masoyan Peter Obi, tsohon gwamnan jihar Anambra, a yanzu su suka fi shahara a kafafen sada zumunta baki ɗaya daga cikin dukkan yan takarar shugaban ƙasa a 2023.

Kara karanta wannan

Wike Ya Saki Hoto Da Magana Mai Boyayyen Ma'ana Bayan Jita-Jitar Ganawarsa Da Tinubu a Faransa

Fasto Oyemade, a rubutunsa wanda ya goge daga baya, ya ayyana goyon bayan da Obi ke samu a Intanet da, "Ɓata lokaci kan aikin da ba'a shirya ba."

A wani labarin kuma Hadimin gwamnan PDP da dandazon magoya baya sun sauya sheƙa zuwa APC, tsohon shugaba ya karɓe su

Tsohon shugaban APC na ƙasa, Kwamaret Adams Oshiomhole, ya karɓi tsohon mashawarcin gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo kan harkokin siyasa, Ogljo Asein, zuwa jam'iyyar APC.

Oshiomhole, tsohon gwamnan jihar Edo, ya yi kira ga 'ya'yan APC a faɗin jihar su haɗa kai wuri guda domin jam'iyyar ta cigaba da mulkin Najeriya a 2023, kana ta kwace mulkin Edo daga hannun PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel