Peter Obi baya kyamar mutanen arewa, karya ake masa: Inji hadimin sa

Peter Obi baya kyamar mutanen arewa, karya ake masa: Inji hadimin sa

  • Hadimin Peter Obi ya ce jam'iyyun adawa suna daukan nauyin cin mutuncin maigidansa a kafofin sadarwa saboda farin jinin sa na karuwa
  • Peter Obi ya bayyana karara cewa arewa na da arzikin filayen noman da zai iya ciyar da Najeriya da kuma kasasen wajen idan sarrafa su yadda ya kamata
  • Peter Obi na cikin manyan yan takara zaben kujerar shugaban kasa uku na gaba da ake sa ran zasu tabuka wani abu

Anambra - Mai Magana da yawun bakin dan tankarar shugabankasa a jam’iyyar Labour party LP, Mista Peter Obi, ya musanta rahoton dake nuna maigidansa mai tsaurin ra'ayin addini ne kuma yana kyamar mutanen arewa.

Valentin Obienyem, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, ya ce wasu kungiyoyi da ba’a san su ba, wadanda ‘yan adawar siyasa ke daukar nauyinsu, ke yada karya kan Obi saboda karuwar farin jininsa.

Kara karanta wannan

Za mu durkusa a gaban Wike idan hakan zai sa ya ci gaba da zama a PDP, in ji Walid Jibrin

Jawabin ya fito ne a lokacin da yake mayar da martini akan wani rahoto dake nuna Mista Obi yaki daukan mataki akan kisan gillar da aka yiwa yan Arewa a watan Maris na shekara 2006 kamar yadda jaridar The Guardian ta rahoto.

PUNCH
Peter Obi baya kyamar mutanen arewa, karya ake masa: Inji hadimin sa
Asali: Twitter

Rahoton ya zargi Obi, wanda, ya zama gwamna daga watan Yuni 2007 zuwa Maris 2014, da umarta hukuma DSS su kori Hausawan dake kasuwanci kusa da gidan sa da kuma korrar wasu yan kasuwan arewa daga wuraren kasuwancin su kamar yadda jaridar The Nigerian News ta rawaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Obienyem ya kara da cewa, Obi mutun ne da ya yadda da hadin kan Najeriya kuma ya yadda da kowani yankin a kasar na da irin gudumawar da zai bada wajen ciyar da kasar gaba.

Obienyem yace:

Kara karanta wannan

Cikakken jerin Sanatoci 58 da aka zazzage, ba za su koma kujerunsu a Majalisar Dattawa ba

“Misali a ziyarar da ya kai wa yankin arewa, Obi ya bayyana karara cewa arewa na da arzikin filaye noma wanda babbar kyauta ce ga Najeriya, wanda idan aka sarrafa ta yadda ya kamata, za ta iya ciyar da al’ummar kasa da kuma fitar da su zuwa kasashen waje.”

Kotu ta yanke wa yan luwadi hukuncin kisa a jihar Bauchi

A bangare guda, kotun shariar musulunci dake jihar Bauchi ta yanke wa wasu matasa biyu da dattijo hukuncin kisa ta hanyar jefewa ranar Laraba, 29 ga watan Yuni, 2022. bisa laifin yiwa wasu kananan yara luwadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel