Matar aure ta haɗa kai da ɗan uwanta sun sace Mijinta kan wata gardama

Matar aure ta haɗa kai da ɗan uwanta sun sace Mijinta kan wata gardama

  • Asirin wata matar aure a Kwara ya tonu yayin da ta ƙulla yin garkuwa da mijinta kan wani sabani da ya shiga tsakanin su
  • Matar mai suna Delu Ali, ta amsa laifinta, ta ce ta yi haka saboda rikicinta da shi game da raba wasu dabbobi a tsakanin su
  • Tuni dai Kotun Majirtire da ke zama a Ilorin ta umarci a garƙame matar a gidan Yari yayin da ta ɗage zaman zuwa 12 ga watan Yuli, 2022

Kwara - An gurfanar da Wata matar aure, Delu Ali, a gaban Kotun Majistire da ke Ilorin babban birnin jihar Kwara bisa zargin ƙulla yadda aka yi garkuwa da Mijinta kan wata gardama da ta haɗa su.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Sanata Ekweremadu ya bayyana a gaban Kotun Birtaniya kan tuhumar yanke sassan jiki

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa matar ta sa an sace Maigidan nata ne kan saɓanin yadda zasu raba wasu shanu a tsakanin su.

An kai ƙarar wata mata da ta sa aka sace mijinta.
Matar aure ta haɗa kai da ɗan uwanta sun sace Mijinta kan wata gardama Hoto: vanguardngr
Asali: Twitter

A cewar jami'in hukumar yan sanda, wasu yan Fulani sun sace Mijin matar mai suna, Alhaji Ali Shehu, a ƙauyen Share da ke ƙaramar hukumar Ifelodun, jihar Kwara.

Ɗan sanda mai shigar da ƙara ya shaida wa Kotun cewa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Yayin da muka tsananta bincike, ya bayyana mana cewa Delu Ali ta haɗa baki da wani ɗan uwanta mai suna, Sanni, wanda har yanzun be shiga hannu ba, suka sa yan bindiga su yi garkuwa da Mijin matar."
"Delu ta amince da shirya garkuwa da Maigidanta kan wata gaddama da ta shiga tsakaninta da shi game da rabon wasu shanu a tsakanin su."

Wane mataki Kotu ta ɗauka?

Kara karanta wannan

Asirin matar aure ya tonu, Mijinta ya fahimci ta ci amanarsa da mutane 9 a boye

Da take yanke hukunci, Alkalin Kotun mai shari'a Folake Olokoyo, ta umarci da a garƙame wacce ake ƙara a gidan Gyaran hali, kuma ta dage sauraron ƙarar zuwa ranar 12 ga watan Yuli, 2022.

Lamarin garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa na ɗaya daga cikin ƙalubalen tsaron da Najeriya ke fama da su musamman a jihohin arewaci.

A wani labarin kuma Wani Alhaji ɗan Najeriya ya maida makudan kuɗin da ya tsinta a jaka a Madinah

Halin kirki a ko da yaushe abun yabo ne, wani maniyyaci ɗan jihar Sokoto ya yi abun a yaba masa yayin da tsinci jaka ɗauke da kudi a Madina.

Mutumin mai suna, Arzika Bakaya, ya tsinci ƙaramar jaka ɗauke da kuɗi amma be wata-wata ba ya kaiwa jami'ai don a maida wa mai ita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel