Matar shugaban NULGE da aka sace a Zamfara ta haihu a hannun 'yan bindiga

Matar shugaban NULGE da aka sace a Zamfara ta haihu a hannun 'yan bindiga

  • Shugaban ma'aikatan kananan hukumomi na jihar Zamfara, Sanusi Isa, ya tabbatar da cewa matarsa ta haihu a sansanin yan bindiga
  • Wasu miyagu sun kutsa har cikin gidan shugaban ƙungiyar NULGE suka yi gaba da matarsa yayin da suka gano baya nan
  • Ya ce matar ta kira shi da lambar wayarta don faɗa masa ta haifi ɗiya mace, tun daga nan bai ƙara samun wayar ba

Zamfara - Ramatu Yunusa, matar shugaban ƙungiyar ma'aikatan kananan hukumomi (NULGE) a Zamfara, Sanusi Isa, wacce aka sace har gida ranar Talata, ta haihu a sasanin yan bindiga.

Shugaban NULGE ya tabbatar da labarin ga jaridar Premium Times a wata zantawa ta wayar salula ranar Alhamis da maraice.

Maharan sun farmaki gidan shugaban ma'aikatan da ke yankin Damba, a babban birnin Zamfara kuma suka yi awon gaba da matarsa da tsohon cikin kasancewar ba su ga mijinta ba.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sako ma'aikatan lafiya, sun maida miliyoyin kuɗin da aka kai musu a Zamfara

Matsalar tsaro a Zamfara.
Matar shugaban NULGE da aka sace a Zamfara ta haihu a hannun 'yan bindiga Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Sanusi Isah ya bayyana cewa mai ɗakinsa ta haifi ɗan jaririnta awanni kaɗan bayan 'yan bindigan sun tafi da ita.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce 'yan bindigan sun kira shi a waya da misalin ƙarfe 5:00 na yammacin ranar Talata domin su shaida masa matarsa ta haifi jariri.

Shugaban NULGE ya ce:

"An kira ni da wayar ta saboda lokacin da suka ɗauke ta sun hada da wayar salulanta. Wajen ƙarfe 5:00 na yama na ga kiran da lambarta na shigowa, na yi zaton zamu tattuana batun kuɗin fansa ne."
"Amma yayin da na ɗaga kiran sai na ji muryarta tana faɗa mun cewa ta sauka lafiya ta haifi mace mintuna kaɗan da suka wuce."

Shugaban NULGE ya ƙara da bayyana cewa har yanzun maharan ba su sake kira ba kuma duk wani yunkuri na samun lambar ya ci tura.

Kara karanta wannan

Wata matar aure ta sa yan bindiga sun yi garkuwa da Mijinta kan wani saɓani tsakanin su

Wane matakin jami'an tsaro ke ɗauka?

Bayan haka Mista Isah ya yaba wa jami'an tsaron jihar Zamfara bisa abinda ya kira namijin kokarin da suke yi domin kuɓutar da matarsa.

"Mun san duk abinda ya faru daga Allah ne kuma na yi imani komai zai wuce bayan halin da na shiga. Ba abinda zance sai godiya ga Allah saboda ni Musulmi ne."

A wani labarin na daban kuma Daruruwan ɗalibai mata sun tsallake rijiya da baya yayin da wuta ta kama rigi-rigi a Hostel ɗinsu a Enugu

Ɗalibai mata sun sha da ƙyar yayin da wata Gobara ta tashi a gidan kwanan su na kwalejin Ilimi ta Peaceland, jihar Enugu.

– Rahoto ya nuna cewa wutar ta fara ne daga ɗaki guda, kuma ta aikata babbar ɓarna da ya haɗa takardun karatun Diplomar ɗalibai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel