Ta tabbata: INEC ta amince da takarar gwamnan Kano ga dan janar Abacha a PDP

Ta tabbata: INEC ta amince da takarar gwamnan Kano ga dan janar Abacha a PDP

  • INEC ta tabbatar da Mohammad Abacha a matsayin dan takarar gwamna na jam'iyyar adawa ta PDP a jihar Kano
  • Wannan ne damar karshe ta yankewa da kawo jita-jita da kai ruwa rana kan wanene sahihin dan takarar gwamnan PDP a Kano tsakanin Mohammed Abacha da Sadiq Wali
  • Muhammad Abacha, dan tsohon shugaban mulkin soja, Sani Abacha, kuma ya zama dan takarar gwamna a PDP a zaben 2023, bayan ya samu kuri’u 36 a zaben fidda gwani

Jihar Kano - Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta tabbatar da cewa ta sa idon basira a zaben fidda gwani da ya samar da Mohammad Abacha a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Za mu durkusa a gaban Wike idan hakan zai sa ya ci gaba da zama a PDP, in ji Walid Jibrin

Kafin bayanin na INEC dai an yi ta cece-kuce kan wanda hukumar za ta amince da shi a matsayin dan takarar gwamna tsakanin Mohammed Abacha da Sadiq Wali.

Mohammed Abacha ne ya lashe zaben fidda gwanin gwamna a Kano
Ta tabbata: INEC ta amince da takarar gwamna ta dan janar Abacha a jihar Kano | Hoto: sunnewsonline.com
Asali: UGC

Kwamishinan zabe na yanki (REC), Farfesa Riskuwa Shehu, ya tabbatar wa manema labarai hakan a Kano, a ranar Alhamis, 30 ga watan Yuni, in ji jaridar The Guardian.

A cewarsa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Kamar yadda a lokacin da aka gudanar da zaben fidda gwani na PDP a Kano, Shehu Sagagi ne wanda doka ta amince da shi a matsayin shugaban jam'iyyar na jiha, haka kuma shi ya gudanar da zaben fidda gwanin da ya samar da Abacha."

Abacha ya kada Wali a zaben fidda gwani

Sai dai, kitimurmurar da aka samu ita ce, Abacha da Wali sun yi nasarar lashe zaben fidda gwani na PDP da aka gudanar a tsagi biyu na PDP a Kano, inda kowannen su ya yi ikirarin cewa shi ne dan takara sahihi.

Kara karanta wannan

Mun Baka Awa 48: PDP Za Ta Yi Wa Obasanjo Fallasa Idan Bai Yi Karin Haske Kan Maganan Da Ya Yi Kan Atiku Ba

Abacha ya samu kuri’u 736 inda ya kayar da babban abokin hamayyarsa, Jafar Sani-Bello, wanda ya samu kuri’u 710 a zaben fidda gwani da aka gudanar a ranar Laraba 25 ga watan Mayu a jihar Kano, kamar yadda a baya Premium Times ta ruwaito.

Zaben 2023: Gwamnatin Neja ta ba da hutun kwanaki 2 don rajista da karbar PVC

A wani labarin, gabanin zaben 2023, Gwamna Abubakar Sani Bello ya ayyana ranar Alhamis 30 ga watan Yuni 2022 da Juma’a 1 ga Yuli 2022 a matsayin ranakun hutu a fadin jihar domin baiwa al’ummar jihar Neja damar mallakar katin zabe na PVC, Channels Tv ta ruwaito.

Gwamnan ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar (SSG), Ahmed Ibrahim Matane ya sanya wa hannu a ranar Alhamis a Minna.

Ya ce hutun, an ba da shi ne don baiwa ma’aikatan gwamnati da masu rike da mukaman gwamnati da kuma ‘yan jihar da suka kai shekaru 18 damar karbar katunansu.

Kara karanta wannan

Jami'in INEC: Kuskure ne Ayyana Machina Matsayin 'Dan Takarar Sanatan Yobe ta Arewa a APC

Asali: Legit.ng

Online view pixel