Atiku ya shiga tsaka mai-wuya a 2023, Fayose ya ce har abada Wike ba zai goyi bayansa ba

Atiku ya shiga tsaka mai-wuya a 2023, Fayose ya ce har abada Wike ba zai goyi bayansa ba

  • Ayo Peter Fayose yana nan a kan bakarsa, yace har abada ba za su goyawa Atiku Abubakar baya ba
  • Tsohon gwamnan na Ekiti ya zargi ‘dan takaran PDP, Atiku Abubakar da cin amanar Nyesom Wike
  • A cewar Fayose, an yi da Atiku zai tafi da Wike amma daga baya sai aka ji ya dauko Ifeanyi Okowa

Lagos - Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Peter Fayose, ya yi bayanin abin da ya sa Nyesom Wike ba zai taba goyon bayan Atiku Abubakar a zaben 2023 ba.

A wata hira da Premium Times ta yi da Ayo Peter Fayose, ya fadi dalilin Gwamna Nyesom Wike na juya baya ga ‘dan takaran na PDP a zaben shugaban kasa.

Fayose ya kara nanata matsayarsa na cewa bayan Muhammadu Buhari ya kammala shekara takwas, abin da ya kamata shi ne shugabanci ya koma kudu.

Kara karanta wannan

Wani shahararren gwamnan PDP: Har yanzu Allah bai yarje min na goyi bayan Atiku ba

Bugu da kari, ‘dan siyasar ya ce Atiku Abubakar ya yi alkawarin zai zabi Gwamnan na Ribas a matsayin abokin takara, amma daga baya ya canza magana.

Atiku ya ci amanar Wike?

An rahoto Fayose yana ikirarin Atiku ya yi wa Wike alkawari shi zai zama ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa bayan gama zaben tsaida gwani.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Daga baya sai aka ji ‘dan takaran ya yi watsi da Gwamna Wike, ya dauko Gwamna Ifeanyi Okowa.

Nyesom Wike
Nyesom Wike da su Atiku Abubakar Hoto: punchng.com
Asali: UGC

“Wike bai taba cewa yana son mataimakin shugaban kasa ba, amma lokacin da Atiku ya kai masa ziyara, shi ne ya ce 'ina so ka zama mataimaki na.'”

“Shi (Atiku) ya fadawa Wike wannan, idan har ya canza magana, shin bai kamata ya sanar da Gwamna Wike ba? Bai dace Wike ya samu labari ba?”

- Ayo Fayose

Kara karanta wannan

Za mu durkusa a gaban Wike idan hakan zai sa ya ci gaba da zama a PDP, in ji Walid Jibrin

Mu na tare da Wike 100%

Ko me zai faru a PDP, tsohon gwamnan ya ce ba zai ci amanar Wike ba, ya ce yana tare da shi dari bisa dari, yake cewar domin da kudin Wike aka tafiyar da jam’iyya.

“An yi wa Wike illa, amma za mu cigaba da zama da shi. Duk abin da ya yi, haka za mu yi; duk inda ya fada mana mu je, can za mu tafi.”
“Wike ba zai taba cewa mu goyi bayan Atiku ba. Na kalubalance shi a kan wannan. Idan Wike ya ce mu bi Atiku, to za mu yi watsi da shi.”

- Ayo Fayose

Ba a dauki maganar kwamiti ba

A hirar da aka yi da shi ta waya, Fayose ya kara da cewa Atiku ya yi watsi da shawarar da kwamitin da PDP ta nada a kan batun takarar 2023, ta gabatar masa.

Kara karanta wannan

Mun Baka Awa 48: PDP Za Ta Yi Wa Obasanjo Fallasa Idan Bai Yi Karin Haske Kan Maganan Da Ya Yi Kan Atiku Ba

“PDP ta kafa kwamiti da zai bada shawarar wa zai zama abokin takara, wanda kwamitin suka zaba shi ne Wike, amma ba ayi aiki da maganar ba.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel