Malami: Mambobin PDP masu yawan gaske na shirin sauya sheka zuwa APC a Kebbi

Malami: Mambobin PDP masu yawan gaske na shirin sauya sheka zuwa APC a Kebbi

  • Ministan shari’a kuma Atoni Janar na tarayya, Abubakar Malami, ya ce akwai mambobin PDP da yawa da ke shirin ficewa daga jam'iyyar zuwa APC
  • Malami ya ce kimanin kaso sittin cikin dari za su sauya sheka daga jam'iyyar adawar zuwa jam'iyya mai mulki a kwanan nan
  • Ya kuma bayyana cewa har gobe shi mai biyayya ne ga Atiku Bagudu da kuma jam'iyyar APC a jihar Kebbi

Kebbi - Ministan shari’a kuma Atoni Janar na tarayya, Abubakar Malami, ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba kaso 60 cikin dari na mambobin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), za su sauya sheka zuwa APC a jihar Kebbi.

Malami ya bayyana hakan ne a Gesse otel da ke Birnin Kebbi a ranar Asabar, 25 ga watan Yuni, yayin wata tattaunawa da kungiyoyi masu goyon bayansa a jihar Kebbi, jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Jerin Sanatocin APC da Suka Sauya Sheka Zuwa PDP da Wasu Jam'iyyu

Abubakar Malami
Malami: Mambobin PDP masu yawan gaske na shirin sauya sheka zuwa APC a Kebbi Hoto: The Guardian
Asali: UGC

Kungiyoyin kimanin su 600 sun hadu don jadadda goyon bayansu ga Malami da jam’iyyar APC reshen Kebbi.

Ministan wanda bai ambaci sunan wadanda za su sauya shekar ba ya kara da cewa an yi tattaunawa mai zurfi kuma tuni aka yi karaye-kiraye don gabatar da su a inuwar APC ba da jamawa ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce:

“Har yanzu biyayyata da goyon bayana ga APC da Bagudu na nan daram-dam, ina mai umartanku da ku mallaki katin zabenku sannan ku zabi APC a 2023.”

Ya yi kira ga kungiyoyin da su ci gaba da goyon bayan APC a jihar Kebbi da ma kasa baki daya.

Taron ya samu halartan manyan jam’iyyar da manyan jami’an gwamnati.

Masu neman takarar gwamna 3 sun sauya sheka daga APC zuwa PDP a jihar Sokoto

A gefe guda, mun ji cewa akalla masu neman takarar kujerar gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben fidda gwanin da aka yi kwanan nan ne suka sauya sheka zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Sokoto.

Kara karanta wannan

Mu na tattaunawa da PDP da ‘Jam’iyyar kayan marmari’ inji ‘Danuwan Buhari, Hon. Fatihu

Daga cikin wadanda suka sauya sheka daga APC zuwa PDP sun hada da wani dan majalisar wakilai, Hon Abdullahi Balarabe Salame, jaridar Punch ta rahoto.

Salame wanda ke wakiltan mazabar Ilella/Gwadabawaa majalisar dokokin tarayya, ya kasance dan majalisa sau uku, sannan ya yi zango biyu a majalisar dokokin jiha, inda ya rike mukamin kakakin majalisa da kuma mukaddashin gwamnan jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel