Peter Obi ya jajantawa Sanatan da aka kama da zargin safarar sassan jikin mutum a Birtaniya

Peter Obi ya jajantawa Sanatan da aka kama da zargin safarar sassan jikin mutum a Birtaniya

  • Kame Ike Ekweremadu da hukumomin Burtaniya suka yi ya mamaye kanun labarai a Najeriya da ma waje cikin sa'o'i 24 da suka gabata
  • An kama dan siyasar wanda haifaffen Enugu ne a kasar Burtaniya bisa zarginsa da ake yi na cire sassan jikin dan adam, kamar yadda hukumomin Burtaniya suka bayyana
  • Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya bayyana damuwarsa kan halin da ‘yar Ekweremadu ke ciki tare da yin addu’ar samun adalci ga iyayenta

FCT, Abuja - Peter Obi ya yi kalaman karfafa gwiwa ga Sanata Ike Ekweremadu da matarsa, Beatrice, kan halin da suke ciki a kasar Birtaniya.

Ekweremadu, wani fitaccen dan majalisar dattawan Najeriya, ya bayyana a wata kotun majistare ta kasar Birtaniya tare da matarsa a ranar Alhamis, 23 ga watan Yuni bisa zargin da ake yi musu na safarar sassan jikin dan adam.

Kara karanta wannan

Har yanzu ban samu wata sanarwa a hukumance daga ubangidana ba - Hadimin Ekweremadu

Peter Obi ya magantu kan kame Ekweremadu
Peter Obi ya jajantawa Sanatan da aka kama bisa zargin yunkurin cire sassan jikin mutum a Birtaniya | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour ya yi la'akari da batun sannan ya yi tsokaci a kai ta shafinsa na Twitter, inda ya bayyana jaje ga tsohon sanatan tare da addu'ar neman lafiya ga diyarsa.

A bangare guda, ya kuma yi rokon tabbatar adalci da fitowar gaskiya a lamarin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A rubutun da ya yi Twitter, Obi ya ce:

“Ni da iyalina muna tare da iyalan Ekweremadu kan halin da suke ciki. Muna hada kai da dukkan masu hannu da shuni wajen yi wa ‘yarsu addu’ar samun lafiya tare da daura su a hannun Allah domin neman adalci.”

An damke Sanata Ekweremadu da matarsa kan yunkurin satar sashen jikin wani yaro

A wani labarin na daban, hukumomi a kasar Birtaniya ta damke tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ike Ekweremadu, da matarsa Beatrice kan laifin kai wani yaro kasar don cire wani sashen jikinsa.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari: Akwai wasu miyagun mutane da ke shirin sanya Najeriya cikin garari

Hukumar yan sandan kasar ta tabbatar da labarin cewa an garkamesu a kurkuku kuma za'a gurfanar da su a kotu ranar Alhamis bayan gudanar da bincike, rahoton Skynews.

Yan sandan sun kara da cewa an kaddamar da bincike ne bayan sanar da su wasu sun kawo dan wani kasar kuma hakan ya sabawa dokar bautar zamani na Birtaniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel