Kwanaki kaɗan bayan ficewa daga PDP, Tsohon minista ya sa labule da gwamna Wike

Kwanaki kaɗan bayan ficewa daga PDP, Tsohon minista ya sa labule da gwamna Wike

  • Kwanaki kaɗan bayan ya yi murabus daga PDP, Tsohon ministan Neja Delta, Chief Orubebe, ya gana da gwamnan Ribas, Nyesom Wike
  • Taron mutanen biyu ya gudana ne a gidan Wike dake Patakwal, babban birnin jihar Ribas kuma a sirrance, ba su ce komai ba bayan fitowa
  • Manyan yan siyasan biyu sun yi aiki karkashin Jonathan kafin daga bisani Wike ya yi murabus ya nemi takarar gwamna a 2015

Rivers - Tsohon ministan harkokin Neja Delta, Chief Godswill Orubebe, ya gana da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ranar Alhamis, 23 ga watan Yuni, 2022 a Patakwal.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa taron manyan yan siyasan biyu ya gudana ne a wani gidan gwamna Wike da ke Patakwal, babban birnin jihar Ribas.

Kara karanta wannan

Bayan tafiyar Peter Obi, Gwamnan Bauchi da wani Jigon PDP sun dira gidan Wike, sun sa labule

Orubebe tare da gwamna Wike.
Kwanaki kaɗan bayan ficewa daga PDP, Tsohon minista ya sa labule da gwamna Wike Hoto: Niger Delta Insider/facebook
Asali: Facebook

Idan baku mance ba kwanaki kaɗan da suka shuɗe, Orubebe ya yi murabus daga kasancewa mamban jam'iyyar PDP don nuna fushinsa ga matakin jam'iyyar na tsayar da ɗan takarar shugaban kasa daga Arewa.

Tsohon Ministan ya zama mutum na huɗu daga cikin fitattun yan Najeriya da suka ziyarci gwamna Wike tun bayan kammala zaɓen fidda gwani.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yayin zaɓen fidda gwanin na jam'iyyar PDP, Wike ya sha kaye a hannun tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Me suka tattauna a taron?

Rahoto ya nuna cewa taron manyan jiga-jigan biyu, Orubebe da Wike, ya gudana ne a sirrance kuma babu ɗaya daga cikin su da ya zanta da manema labarai bayan kammala taron.

Legit.ng Hausa ta tattaro muku cewa idan zaku iya tunawa Chief Orubebe da Wike sun yi aiki tare a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Dakta Goodluck Jonathan.

Kara karanta wannan

Da walakin goro a miya: Jerin yan siyasa 2 da ba yan PDP da suka gana da Wike a cikin mako 1

Amma daga bisani Wike ya yi murabus daga muƙaminsa domin ya samu damar neman takarar gwamna a babban zaben 2015 karkashin inuwar jam'iyyar PDP.

A wani labarin kuma Bayan tafiyar Peter Obi, Gwamnan Bauchi da wani Jigon PDP sun dira gidan Wike, sun sa labule

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi da Mataimakin shugaban APC na shiyyar kudu maso kudu, Chief Dan Orbih, yanzu haka sun shiga ganawar sirri da gwamnan Ribas, Nyesom Wike.

Babban mai taimaka wa gwamnan Bauchi ta ɓangaren Midiya, Kelvin Ebiri, shi ya tabbatar da haka ga jaridar Leadership a Patakwal, babban birnin Ribas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel