Da walakin goro a miya: Jerin yan siyasa 2 da ba yan PDP ba da suka gana da Wike a cikin mako 1

Da walakin goro a miya: Jerin yan siyasa 2 da ba yan PDP ba da suka gana da Wike a cikin mako 1

  • Jita-jita da ake yi na shirin ficewar gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike daga jam’iyyar PDP na kara kamari
  • Wike dai ya saka labule da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na NNPP da Peter Obi na Labour Party a cikin mako daya
  • Lamarin na zuwa ne bayan Atiku Abubakar ya yanke shawarar kin zabar gwamnan na jihar Rivers a matsayin mataimakinsa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

A yayin da ake tsaka da yada jita-jitan cewa Gwamna Nyesom Wike na shirin ficewa daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), babban dan siyasan na jihar Ribas na ta ziyartan yan siyasa daga sauran jam’iyyun siyasa, lamarin da ya kara rura wutar rade-radin.

Wannan hasashen na zuwa ne tare da batun cewa gwamnan ya fusata ne kan sakamakon zaben fidda gwanin shugaban kasa na PDP da kuma hana shi tikitin mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar a zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Da dumi-duminsa: Peter Obi ya ziyarci Gwamna Nyesom Wike a Port Harcourt

Legit.ng ta tattaro wasu hotuna wadanda a ciki aka gano Wike tare da yan takarar shugaban kasa na jam’iyyun New Nigerian Peoples Party, Rabiu Kwankwaso, da Labour Party, Peter Obi.

Nyesome Wike tare da Rabiu Kwankwaso, Peter Obi
Da walakin goro a miya: Wike ya ziyarci Peter Obi da Kwankwaso cikin mako 1 Hoto: @delemomodu/@OkoyeCardinal
Asali: Twitter

Wannan ziyara ya jefa masu lura da lamuran siyasa cikin al’ajabin abun da tsohon dan takarar shugaban kasar na PDP yake kitsawa a zuciyarsa idan har yana tunanin sauya sheka ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Peter Obi ya ziyarci Gwamna Nyesom Wike a Port Harcourt

A baya mun kawo cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP), Mista Peter Obi, ya ziyarci gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike a Port Harcourt a ranar Laraba, 22 ga watan Yuni.

Legit.ng ta tattaro cewa sun shafe tsawon awanni suna saka labule a tsakaninsu a gidan Gwamna Wike da ke Port Harcourt, babban birnin jihar Rivers.

Kara karanta wannan

Atiku ya tura manya su yi wa Wike danniyar kirji domin gudun a samu cikas a 2023

Ana dai ta rade-radin cewa Wike na shirin ficewa daga jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP bayan ya fadi a zaben fidda gwanin jam’iyyar sannan kuma aka ki zabarsa a matsayin abokin takarar Atiku Abubakar, wanda zai daga tutar jam’iyyar a zaben shugaban kasa na 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel