Takaitaccen tarihin mutum 7 da Buhari ya zaba domin su zama sababbin Ministocinsa

Takaitaccen tarihin mutum 7 da Buhari ya zaba domin su zama sababbin Ministocinsa

  • A ranar Talata, 21 ga watan Yuni 2022, aka ji cewa Muhammadu Buhari ya aika sunayen Ministoci
  • Idan an tabbatar da wadannan mutane bakwai, za su maye guraben Ministocin da suka ajiye aikinsu
  • Sunayen wadanda aka aika sun hada da shugaban OGFZA da tsohon shugaban majalisa na jihar Imo

1. Henry Ikechukwu

Henry Ikechukwu ya rike Kwamishinan masana’antu a gwamnatin Okezie Ikpeazu. Daga baya ya fice daga PDP zuwa APC, ya nemi mataimakin shugaban jam’iyya.

Ikechukwu ya fito ne daga kauyen Ahuwa Oboro a garin Ikwuano, jihar Abia. ‘Dan siyasar ya yi sha’awar tsayawa takarar Sanatan Abia ta tsakiya a APC a zaben 2023.

2. Umana Okon Umana

Umana Okon Umana shi ne wanda ya yi wa APC takarar gwamnan Akwa Ibom a zaben 2015, amma ya sha kashi a hannun Udom Emmanuel da PDP ta tsaida.

Daga baya Muhammadu Buhari ya nada shi shugaban hukumar OGFZA mai kula da sha’anin harkar mai da gas. A 2019 aka kara masa wa’din shekaru uku.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

3. Umar Ibrahim El-Yakub

Hon. Umar Ibrahim El-Yakub shi ne Mai ba shugaban Najeriya shawara a kan harkokin majalisar wakilan tarayya tun bayan tafiyar Abdulrahman Kawu Sumaila.

Kafin yanzu Ibrahim El-Yakub ya taba zama ‘dan majalisar tarayya inda ya wakilci mazabar Birnin Kano da kewaye a jihar Kano daga shekarar 1999 zuwa 2007.

Shugaba Buhari
Buhari ya na sa hannu a kasafin kudi Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

4. Goodluck Nanah Opiah

Rt. Hon. Chief Goodluck Nanah Opiah rikakken ‘dan siyasa ne wanda ya fito daga Abacheke Egbema, a 2007 ya zama shugaban majalisar dokokin jihar Imo.

Kafin yanzu Goodluck Opiah ya wakilci Ohaji/Egbema, Oguta, Oru a majalisar tarayya, shi ne Mai ba gwamna Hope Uzodinma shawara a kan harkar gas da mai.

5. Ekuma Joseph

Ekume Joseph shi ne wanda Mai girma Muhammadu Buhari ya zaba domin ya maye gurbin Ogbonnoya Onu daga jihar Ebonyi a majalisar FEC ta Ministoci.

Joseph ya taba zama Mai ba Gwamnan Ebonyi, David Umahi shawara na musamman. Daga baya aka nada shi a matsayin Kwamishina har zuwa Mayun 2021.

6. Ademola Adewole Adegorioye

Zaman Ademola Adewole Adegorioye Minista zai tabbatar da cewa Tayo Alasoadura ya yi biyu-babu bayan da ya ajiye kujerarsa, ya kuma rasa takarar Sanata a Ondo.

Legit.ng ta fahimci Ademola Adegorioye ya nemi zama 'dan majalisar tarayya na yankin Akure.

7. Odo Udi

Idan majalisa ta tantance Odo Udi, zai wakilci jihar Ribas a FEC. Zabinsa ya ba mutane mamaki domin ana tunanin Rotimi Amaechi ne zai sake komawa kujerarsa.

Udi ya rike shugaban karamar hukumar Abua Odua a Ribas a lokacin Amaechi yana Gwamna a 2008, ya kuma samu damar zarcewa a kan wannan kujera a 2011.

Abokin takarar Tinubu

Ku na da labari cewa wasu Matasa sun ba ‘Dan takaran APC, Asiwaju Bola Tinubu shawarar wanda ya kamata ya zama Mataimakinsa a zaben shugaban kasa.

'Yan North East All Progressive Congress Enlightenment Circle sun yi watsi da su Kashim Shettima da Gwamnoni masu-ci, sun bada sunan Abubakar Malami.

Asali: Legit.ng

Online view pixel