Yanzu-Yanzu: Buhari ya kai sunayen mutum 7 majalisa don su maye gurbin wasu ministocinsa

Yanzu-Yanzu: Buhari ya kai sunayen mutum 7 majalisa don su maye gurbin wasu ministocinsa

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sunayen wasu jami'ai bakwai da za su maye wasu ministocinsa
  • A baya an samu wasu daga cikin ministocin Buhari da suka bayyana murabus saboda su tsaya takara a 2023
  • Bayan wannan, an ja lokaci kafin yau, lokacin da Buhari ya mika sunayen wadanda za su maye gurbinsu ga majalisa

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rubutawa majalisar dattawa wasika yana neman a tantance sunayen ministoci bakwai, Channels Tv ta ruwaito.

Wannan na zuwa ne tun bayan da wasu daga cikin ministocin nasa suka yi murabus tare da tsayawa takarar kujerun takara a kasar nan.

Buhari ya mika sunayen sabbin ministocinsa
Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari ya mika sunayen sabbin ministocinsa da za su maye su Amaechi | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Wadanda Buhari ke son nadawa sune:

  1. Henry Ikechukwu – Jihar Abia
  2. Umana Okon Umana – Jihar Akwa-Ibom
  3. Ekuma Joseph – Jihar Ebonyi
  4. Goodluck Nana Obia – Jihar Imo
  5. Umar Ibrahim Yakubu – Jihar Kano
  6. Ademola Adewole Adegorioye – Jihar Ondo
  7. Odo Udi – Jihar Ribas

Kara karanta wannan

Ku san tarihin mutum 7 da Shugaba Buhari ya zaba domin su rike masa kujerar Minista

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Majalisar Dattawa, duk da haka, ba ta tsayar da ranar da za a gudanar da aikin tantancewar ba tukuna.

Majalisar dattawa ta nada sabon shugaban marasa rinjaye

A ranar Talata ne majalisar dattawa ta nada Sanata Philip Tenimu Aduda (FCT) a matsayin sabon shugaban marasa rinjaye na majalisar, The Nation ta ruwaito.

Haka kuma an nada Sanata Chukwuka Utazi a matsayin bulaliyar marasa rinjaye a majalisar dattawa.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ne ya sanar da nadin yayin da yake karanta wasiku daban-daban guda biyu dauke da sa hannun sakataren jam’iyyar PDP na kasa Samuel Anyanwu.

Zaben 2023: Abokin takarar Tinubu na wucin gadi zai iya jefa shi cakwalkwali, hasashen masana a INEC

A wani labarin, tsoffin daraktocin hukumar zabe mai zaman kanta da kuma masu hasashe a Najeriya sun yi gargadin cewa jam’iyyun siyasa na iya fuskantar rikici kan zaben fitar da gwanin da suka yi da kuma zabo abokan takarar a zaben shugaban kasa na 2023.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Majalisar dattawa ta nada sabon shugaban marasa rinjaye

Tsofaffin jami’an alkalan zaben, wadanda suka zanta da jaridar Punch, sun gargadin cewa jam’iyyu da ‘yan takararsu na iya gamuwa da tasgaron rashin nasara a zaben shugaban kasa, idan wanda aka zaba a matsayin abokin takaran wucin gadi ya ki amincewa a sauya shi.

Wani batu da tsofaffin jami’an hukumar zabe ta INEC suka yi shi ne cewa jam’iyyu da ‘yan takararsu na iya rasa tikitin takara idan abokin takarar da bai cancanci zama mataimakin shugaban kasa ba ya ki janyewa daga takarar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel