APC ta sake rasa Sanata da wasu Jiga-jigan ‘Yan siyasa zuwa NNPP a jihar Bauchi

APC ta sake rasa Sanata da wasu Jiga-jigan ‘Yan siyasa zuwa NNPP a jihar Bauchi

  • Jam’iyyar NNPP ta ribato Sanatan jihar Bauchi ta tsakiya a Majalisar Dattawa, Halliru Dauda Jika
  • Sanata Halliru Dauda Jika ya fice daga APC bayan shan kashi a zaben zama ‘dan takarar Gwamna
  • Arch. Audu Sule Katagum yana cikin jagororin da jam’iyyar APC ta rasa a jihar ana shirin zaben 2023

Bauchi - Sanata mai wakiltar mazabar Bauchi ta tsakiya a majalisar dattawa, Halliru Dauda Jika ya fice daga jam’iyyar APC mai rinjaye a majalisa.

Solacebase ta kawo rahoto a ranar Lahadi, 19 ga watan Yuni 2022, Sanata Halliru Dauda Jika ya sauya-sheka ne zuwa jam’iyyar hamayya ta NNPP.

Sanatan ya shaidawa Duniya wannan mataki da ya dauka a wata wasika da ya aikawa shugaban APC na mazabar Kafin Madaki a garin Ganjuwa.

Kara karanta wannan

Tarihin ‘Dan takaran Yobe da ya karya lakanin Ahmad Lawan, ya sa shi yin biyu-babu

Wasikar ta shiga hannun jam’iyyar APC mai adawa a jihar Bauchi ne a ranar Alhamis da ta wuce.

Halliru Dauda Jika ya godewa shugabannin APC da suka ba shi dama ya nemi takarar kujerar gwamna a zaben fitar da gwanin da aka yi kwanaki.

Takarar Gwamna a APC

Jaridar The Gazette ta ce Sanata Jika ya shiga jam’iyyar NNPP ne bayan ya gagara zama ‘dan takarar gwamnan jihar Bauchi a APC a zabe mai zuwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Air Marshal Sadique Abubakar (mai ritaya) ya doke Sanata Jika a zaben tsaida ‘dan takarar gwamna. Abubakar ya samu kuri’a 370, Jika ya ci 278.

Kwankwaso
Jagororin NNPP tare da tsohon Gwamnan Bauchi Hoto: @SaifullahiHon
Asali: Twitter

Wata majiya ta ce magoya bayan Sanatan mai shekara 46 suka dage a kan cewa ya koma NNPP bayan ya rubuta takardar da ta tabbatar da barinsa APC.

NNPP ta kara karfi a Bauchi

Kara karanta wannan

Rikici ya kunnowa APC, ‘Yan adawa na iya karbe Jihar Shugaban kasa a zaben 2023

Jika shi ne Sanata na biyu da ya shiga jam’iyyar ta NNPP daga APC a ‘yan majalisar Bauchi. Kafin nan, Lawan Yahaya Gumau ya shiga jam’iyyar hamayyar.

Sauran ‘yan APC na jihar Bauchi da suka sauya-sheka sun hada da Audu Sule Katagum wanda ya rike mataimakin gwamna a jihar a gwamnatin da ya wuce.

Sauya-shekar ta na nufin NNPP ta samu karin magoya baya a kananan hukumomin Ganjuwa, Katagum da sauran inda ‘yan siyasar ke da magoya-baya.

Lawan Yahaya Gumau ya bar APC

Kwanaki kun ji labari Sanata Lawan Yahaya Gumau ya shiga jam’iyya mai kayan marmari. Gumau shi ne mai wakiltar kudancin jihar Bauchi a majalisa.

Bayan ya fice daga APC mai mulkin Najeriya da rinjaye a majalisar dattawa, Sanatan bai yi wata-wata ba, ya yanki fam a jam’iyyar NNPP domin ya sake takara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng