Shugaban kamfe ya kyankyasa inda Abokin takarar Tinubu zai fito daga Jam’iyyar APC

Shugaban kamfe ya kyankyasa inda Abokin takarar Tinubu zai fito daga Jam’iyyar APC

  • Abdulazeez Yinka-Oniyangi ya ce yawan kuri’u za a duba wajen fito da abokin takarar Bola Tinubu
  • Wannan ne babban abin da za a duba tsaida ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa a APC a 2023
  • Oniyangi ya ce Musulmai ba su da rinjaye a Kudu, don haka dole APC ta dauko Musulmin Arewa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Abdulazeez Yinka-Oniyangi wanda yana cikin shugabannin kwamitin yakin neman zaben Bola Ahmed Tinubu ya tabo batun abokin takara.

Da Daily Trust ta yi hira da Abdulazeez Yinka-Oniyangi a wani shirin siyasa, ya ce kuri’a za a duba wajen zaben mataimakin Bola Ahmed Tinubu a zaben 2023.

Da yake bayani a ranar Juma’a, 17 ga watan Yuni 2022, shugaban kwamitin yakin zaben na shiyyar Arewa maso tsakiya ya ce APC ta na da lokaci.

Kara karanta wannan

Gwamna Okowa ya yi magana kan dalilin daukarsa da Atiku ya yi maimakon ya zabi Wike

Sai nan da 15 ga watan Yuli sannan hukumar INEC za ta daina karbar canjin sunan ‘yan takara.

Kabiru Ibrahim Masari

Kafin wannan lokaci ne Bola Tinubu zai cire sunan Kabiru Ibrahim Masari da ya mikawa hukumar INEC, ya maye gurbinsa da wanda ya dauko.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Oniyangi yake cewa bada sunan Kabiru Masari da aka yi, bai nufin APC ba ta shirya ba, ya ce an yi hakan ne saboda sai sun yi la’akari da wasu abubuwa.

'Dan takaran APC
'Dan takaran APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Musulmi da Musulmi?

Har ila yau, Yinka-Oniyangi ya shaidawa gidan talabijin cewa jam’iyyar APC ba za ta samu kanta a matsala a 2023 idan ta tsaida Musulmi da Musulmi ba.

“Ko ka ki, ko ka so, shi [Tinubu] ya san harkar siyasa. Saboda mu na cikin manyan jam’iyyun siyasa biyu, maganar yawan kuri’u ake yi.”

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Tinubu ya zabi Musulmi a matsayin abokin tafiyarsa a zaben 2023 a APC

“Tinubu yana cikin rukunin Musulmai marasa rinjaye a yankinsa, zai fi bada ma’ana sai a nemi kuri’a, abin da ke gabanmu shi ne nasara.”
“Bugu da kari, wadannan biyun; Atiku da Tinubu tsofaffin ‘yan siyasa ne da suka goge.”

- Abdulazeez Yinka-Oniyangi

Jagoran na tafiyar Bola Tinubu yake cewa babu abin da APC za ta iya yi illa a zabowa ‘dan takarar shugaban kasar abokin takararsa daga Musulman Arewa.

“A wurinmu, yawan kuri’a shi ne a gaba, amma dole mu yi ta-ka-tsan-tsan a kan abin da za mu yi.

- Abdulazeez Yinka-Oniyangi

Zaben Ekiti

Rahoto na kai-tsaye da mu ka fitar ya bayyana cewa Abiodun Oyebanji mai takarar gwamnan Ekiti a jam’iyyar APC ya yi galaba a kan abokan adawarsa.

Abiodun Oyebanji ya samu kuri’a sama da 187, 000 a zaben sabon gwamnan da aka gudanar. Jam’iyyar SDP ce wanda ta zo na biyu, PDP ta kare a ta uku.

Kara karanta wannan

Ana kishin-kishin, Tinubu ya nuna wanda yake so ya zama Mataimakinsa a zaben 2023

Asali: Legit.ng

Online view pixel