Bidiyo da Hotunan Shagalin da ya Barke a Gidan Oyebanji, Bagudu, Badaru da Wasu 'Yan Siyasa Sun ziyarcesa

Bidiyo da Hotunan Shagalin da ya Barke a Gidan Oyebanji, Bagudu, Badaru da Wasu 'Yan Siyasa Sun ziyarcesa

  • Magoya baya da masoyan sabon zababben gwamnan jihar Ekiti, Abiodun Oyebanji, sun cika gidansa dankam inda ake ta kade-kade da raye-raye
  • An sanar da nasararsa ta lashe zaben gwamnan Ekiti a ranar Lahadi, lamarin da ya jefa masoyansa cikin murna da farin ciki
  • Daga cikin wadanda suka dira gidansa akwai, Gwamna Badaru, Gwamna Bagudu, Gwamna Kayode Fayemi da Otunba Niyi, ministan Buhari

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Ekiti - Magoya bayan sabon gwamnan jihar Ekiti, Abiodun Oyebanji na jam'iyyar APC sun fada tsananin murna, annashuwa tare da shagali a ranar Lahadi yayin da abokansa na siyasa, magoya baya da 'yan uwa suke ta taururuwar zuwa gidansa domin taya shi murnar nasarar da ya samu a zaben gwamnan jihar Ekiti da aka yi.

Bidiyoyi da hotunan yadda jama'a ke ta murna sun bayyana inda ake ta busa tare da kade-kade har da rawa a gidan Oyebanji.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Atiku Abubakar ya Zabi Gwamna Okowa a Matsayin Abokin Tafiyarsa

Magoya Bayan Biodun Oyebanji Suna Murnar Cin Zabensa
Bidiyo da Hotunan Shagalin da ya Barke a Gidan Oyebanji, Bagudu, Badaru da Wasu 'Yan Siyasa Sun ziyarcesa. Hoto daga vanguardngr.com
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga cikin manyan 'yan siyasan da aka gani a bidiyon sun hada da Gwamna Abubakar Badaru na jihar Jigawa, shugaban kungiyar gwamnonin APC, Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi, Gwamna Kayode Fayemi da ministan masana'antu kasuwanci da hannayen bari, Otunba Niyi Adebayo.

Vanguard ta ruwaito cewa, wani hoto ya nuna lokacin da Fayemi ya mika sakamakon zaben da takardar shaidan zuwa ga wanda zai gaje shi, Oyebanji.

Magoya Bayan Oyebanji Suna Murnar Nasararsa
Bidiyo da Hotunan Shagalin da ya Barke a Gidan Oyebanji, Bagudu, Badaru da Wasu 'Yan Siyasa Sun ziyarcesa. Hoto daga vanguardngr.com
Asali: UGC

Magoya Bayan Oyebanji Suna Murnar Nasararsa
Bidiyo da Hotunan Shagalin da ya Barke a Gidan Oyebanji, Bagudu, Badaru da Wasu 'Yan Siyasa Sun ziyarcesa. Hoto daga Vanguardngr.com
Asali: UGC

Asali: Legit.ng

Online view pixel