Da duminsa: APC ta Lashe Zabe a Karamar Hukuma ta Farko a Ekiti

Da duminsa: APC ta Lashe Zabe a Karamar Hukuma ta Farko a Ekiti

  • 'Dan takarar gwamnan jihar Ekiti a karkashin jam'iyyar APC, Abiodun Oyebanji ya lashe zabe a karamar hukumar Ikere ta jihar
  • Oyebanji ya yi nasarar samun kuri'u 12,086, yayin da Bisi Kolawole na jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 3,789, sai Segun Oni na SDP mai kuri'u 1,934
  • Sakamakon karamar hukumar Ikere ta jihar Ekiti ya fito ne daga cibiyar tattara sakamakon zabe ta jihar kamar yadda suka sanar

Ekiti - Jam'iyyar APC mai mulki ta tabbata wacce ta lashe zaben gwamna jihar Ekiti da ake yi na karamar hukumar Ikere ta jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Kamar yadda sakamakon da aka sanar ya bayyana daga cibiyar tattara sakamakon zaben, Abiodun Oyebanji na jam'iyyar APC ya samu kuri'u 12,086, 'dan takarar jam'iyyar PDP, Bisi Kolawole ne ke biye da shi wanda ya samu kuri'u 3,789 yayin a Segun Oni na jam'iyyar SDP ya samu kuri'u 1,934.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Kwankwaso ya zabi Barista Ladipo Johnson matsayin mataimakinsa

Jam'iyyar APC ta lashe zabe a karamar hukuma ta farko a Ekiti
Da duminsa: APC ta Lashe Zabe a Karamar Hukuma ta Farko a Ekiti
Asali: Original

Karin bayani na nan tafe...

Asali: Legit.ng

Online view pixel