Matata Ta Roke Ni In Raba Wa Daligets Kudi, In JI Dan Takarar Shugaban Kasa Na Jam'iyyar ADC, Kachikwu

Matata Ta Roke Ni In Raba Wa Daligets Kudi, In JI Dan Takarar Shugaban Kasa Na Jam'iyyar ADC, Kachikwu

  • Dumebi Kachikwu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC ya ce wasu daligets sun yi fushi da shi saboda bai raba musu kudi ba
  • Kachikwu ya kuma ce a safiyar ranar zaben fidda gwanin matarsa ta roke shi ya raba wa daligets din kudi don kada ya ji kunya a yayin zaben
  • A cewarsa, rabon kudin bai dace da tsarin rayuwarsa ba don haka ya dangana da Allah kuma duk da haka ya yi nasarar cin galaba kan wadanda suka raba kudin

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar African Democratic Party kuma shugaban Roots TV, Dumebi Kachikwu, a ranar Laraba ya bayyana cewa matarsa ta roke shi ya bawa daligets toshiyar baki don gudun abin kunya a zaben fidda gwani na shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Dan takarar shugaban kasa: Mata ta ta so na jika deliget da kudi, na ki, kuma na ci zabe

Ya ce duk da cewa bai kashe ko sisi ba don bawa daligets toshiyar baki kafin zaben, ya yi mamakin ganin ya yi nasara kan yan takarar da suka raba wa daligets kudi, The Punch ta rahoto.

Dumebi Kachukwu.
Matata Ta Roke Ni in Raba Wa Daligets Kudi, in JI Dan Takarar Shugaban Kasa Na Jam'iyyar ADC, Kachukwu. Hoto: @MobilePunch.
Asali: Twitter

Kachikwu ya bayyana hakan ne yayin da ya ke magana da manema labarai a Abuja. Ya kuma ce bayan ya yi nasara, ya kira wani daya cikin wanda suka fafata amma bai daga wayarsa ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

"Na yi taro da dukkan daligets, na fada musu ni dan takara ne amma ba ni da kudi don haka su zabi wanda ya kwanta musu a rai, idan na ci zabe hankali zai kwanta ba kudi na biya ba.
"Idan ban ci ba, zan koma kasuwanci na. Ba sai na zama shugaban kasa zan yi wa Najeriya aiki ba. Na bar su a daren, ban san abin da zai faru ba.

Kara karanta wannan

Ban hakura ba fa: Zan sake tsayawa takarar shugaban kasa, in ji Yaha ya Bello

"Na fada musu ba zan bawa kowa kudi ba. Wasu sun fusata, na tafi ban san abin da zai faru da ni ba. Abokan hammaya na sun raba kudi. Bayan kwana guda, matata ta ce min, 'don Allah, ka bawa daligets kudin nan don gudun abin kunya, kana da shi' amma na fada mata zuciya na bai kwanta da hakan ba. Na zaci ba zan kai labari ba. Na fara jawabin amincewa da shan kaye sai na ga yanayin daligets din ya canja. Sun min murmushi.
"Abin takaici shine wadanda suka sha kaye sun tafi gidajen watsa labarai suna karya kan yadda aka yi zaben. Suna yi wa al'umma karya."

Kachikwu ya ce son kai ne ya yi wa yan Najeriya yawa kuma akwai bukatar a canja yadda mutane ke tunani da yin abubuwa.

Ekiti 2022: 'Idan Ba Kuri'a, Ba Kudi', Bidiyon Tinubu Yana Yi Wa Masu Zabe Ba'a a Wurin Kamfen

Kara karanta wannan

Mataimakin shugaban kasa: Daga karshe Tinubu ya fayyace gaskiyar lamari kan tikitin Musulmi da Musulmi

A wani rahoton, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a zaben 2023, Asiwaju Bola Tinubu, ya bukaci al'ummar Jihar Ekiti su fito su yi zabe idan ba hakan ba ba za a biya su ba.

Tinubu, wanda ya ziyarci a Jihar Ekiti a ranar Talata ya furta hakan ne wurin yakin neman zabe na dan takarar gwamna na jam'iyyar, Biodun Oyebanji gabanin zaben da ake shirin yi ranar Asabar 18 ga watan Yunin 2022.

Ya kuma kambama kansa cewa bai taba fadi zabe ba a baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel